Gwamnatin Tinubu Ta Gano Talakawan da Suka Fi Bukatar Taimako a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta ce ta kammala tattara bayanan mutanen da suka fi fama da talauci da matsin rayuwa a rijistar marasa galihu
- Ministan harkokin jin kai, Dr. Bernard Doro ya ce sun bi ka'idoji da taimakon al'umma wajen gano talakawan da suka fi fama da talauci
- Doro ya ce rijistar da gwamnati ta hada a yanzu, na kunshe ne da talakawan da suka fi bukatar taimako a fadin kasar nan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na ci gaba xa kokarin yakar talauci a Najeriya.
Gwamnatin ta yi ikirarin cewa zuwa yanzu, ta kammala gano mutanen da suka fi ko wadanne fama da talauci da kuncin rayuwa.

Source: Twitter
Ministan Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci, Dr. Bernard Doro, ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a cikin shirin 'The Morning Show' na tashar Arise TV a ranar Juma’a, 13 ga watan Fabrairu, 2026.
Gwamnatin Tarayya ta hada bayanan talakawa
Dr. Doro ya bayyana cewa gwamnatin Tarayya ta yi nasarar gano gidaje mafi talauci a Najeriya ta hanyar rijistar jin-ƙai ta ma’aikatarsa.
Ministan ya ce tsarin tantancewar da aka yi amfani da shi a aikin hada rijistar, ya dogara sosai da bayanan al’umma wajen gano waɗanda suka fi buƙatar taimako a fadin kasar nan.
Ya jaddada cewa ba duk talakawan Najeriya ne aka saka a rijistar ba, domin tsarin ya fi mayar da hankali ne kan “mutanen da suka fi fana da talauci a cikin talakawa."
Yadda aka hada rijistar talakawan Najeriya
A cewarsa, rijistar jin-ƙai a halin yanzu ta ƙunshi bayanan gidaje marasa galihu miliyan 17.9, wanda ke wakiltar kimanin ’yan Najeriya miliyan 70.
“An hada rijistar ne tare da haɗin gwiwar al’umma. Galibi mun fi dogaro da bayanan da muka samu daga al’umma, ta hanyar amfani da ka’idojin tattalin arziki da zamantakewa.
"Ta haka muka bi muka hada bayanan waɗanda suka fi buƙatar taimako daga cikin talakawa a fadin kasar nan,” in ji Doro.

Source: Twitter
Ya ƙara da cewa al’umma na taka muhimmiyar rawa wajen bai wa ma’aikatar bayanan masu karamin karfi domin tabbatar da cewa tallafi ya kai ga waɗanda suka fi cancanta.
Wani magidanci, Malam Kabiru Yusuf ya shaidawa Legit Hausa cewa babu amfanin wannan rijistar matukar ba tallafawa talakawan za a yi ba.
Ya ce mutane na cikin wahala da talauci, wanda ya samo asali daga tsare-tsaren gwamnati mai ci, kamar cire tallafin man fetur.
"Tattara bayanan talakawan da suka fi fama da talauci bai da amfani idan ba za a kawo tsare-tsaren da zasu tsamo su daga talauci ba, mutane na shan wahala tun bayan cire tallafi.
"Idan ana son a taimaki talaka to saukaka masa farashin kayan amfani na yau da kullum kuma a samar masa da hanyoyin neman na kansa," in ji shi.
Gwamnatin tarayya ta bullo da sabon shiri
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da sabon shirin horaswa kyauta a fadin kasa domin ba ’yan Najeriya miliyan 10 ilimin hada-hadar kudi.
Rahotanni sun nuna cewa ofishin mataimakin shugaban kasa ne ke jagorantar shirin ta hannun kwamitin shugaban kasa kan tattalin arziki,
Rahotanni sun nuna cewa an tsara shirin ne domin bai wa mata da matasa kwarewa a harkar kudi, zuba jari da dabarun habaka tattalin arziki
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


