Mutane na cikin Hada Hada, Gobara Ta Sake Kamawa Rigi Rigi a Fitacciyar Kasuwa a Kano

Mutane na cikin Hada Hada, Gobara Ta Sake Kamawa Rigi Rigi a Fitacciyar Kasuwa a Kano

  • A karo na biyu cikin kasa da makonni biyu, kasuwar Singa da ke cikin jihar Kano ta sake fuskantar ibtila'in gobara yau Asabar
  • Rahotanni daga yan kasuwa sun nuna cewa gobarar ta kama ne a sashen Gidan Glass da misalin karfe 4:00 na yamma
  • Babu wata sanarwa a hukumance kawo yanzu amma majiyoyi sun tabbatar da cewa motar 'yan kwana-kwada daya kacal ta ka dauki kasuwar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Rahotanni sun nuna cewa 'yan kasuwa sun sake gamuwa da ibtila'in gobara a fitacciyar kasuwar nan ta Singa da ke cikin birnin Kano.

An ruwaito cewa gobarar ta lalata shaguna da dama a sashen Gidan Glass na kasuwar da ke kan titin Ado Bayero, kusa da Murtala Muhammad Way.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 200 sun shiga garuruwa 3 da Asubah, sun kashe mutane sama da 30

Jihar Kano.
Taswirar jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin, wanda ya fara da yammacin ranar Asabar, 14 ga watan Fabrairu, 2026, shi ne karo na biyu da gobara ke tashi a kasuwar cikin ƙasa da makonni biyu.

Gobara ta kama a kasuwar Singa

Wani ɗan kasuwa, Nasir Maharazu, ya shaida wa manema labarai cewa gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, kuma har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto, wutar na ci gaba da ci a Singa.

Ya ce:

“Yanzu da nake magana da ku, ina ganin wutar tana ci. Dukkan ginin bene mai hawa biyu ya kama da wuta. Wannan gobara ma ta fi wadda ta tashi a kasuwar cikin makonni biyu da suka gabata muni.”

Kara karanta wannan

Samha Inuwa: Kotu ta yanke wa fitacciyar jarumar Kannywood hukuncin ɗaurin wata 6

Me ya haddasa gobara a Singa?

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa gobarar ta samo asali ne daga wani shagon sayar da kayan masarufi, inda aka ga hayaƙi mai kauri ya mamaye sararin samaniya tare da haddasa ruɗani a cikin kasuwar da ke cike da jama’a.

An ga ‘yan kasuwa da mazauna yankin suna ƙoƙarin ceto kayayyakinsu da kuma hana wutar yaɗuwa zuwa gine-ginen da ke kusa.

Wani shaida ya ce:

“Gobarar ta fara ne daga wani shagon kayan masarufi. Cikin ƴan mintuna kaɗan, ta yaɗu zuwa wasu shaguna. Mun yi ƙoƙarin fitar da wasu kayayyaki, amma zafin wuta da hayaƙin sun yi yawa.”

Jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano sun isa wurin da motar kashe gobara, amma an ruwaito cewa ruwan da suka zo da shi ya ƙare yayin da suke ƙoƙarin shawo kan wutar, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Bayan janye 'yan sanda daga gadin manya, gwamnatin Tinubu ta fadi inda ta kai su

Gwamna Abba.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabur Yusuf a gidan gwamnati Hoto: Sanusi Bature
Source: Facebook

An bukaci gwamnatin Kano ta dauki mataki

Wani da ya je kasuwar a wannan rana, Aminu Sulaiman ya tabbatar wa Legit Hausa cewa gobarar ta tashi ne cikin kankamin lokacin, kafin a ankara ta yadu zuw shaguna.

"Ba na kusa da wurin sanda gobarar ta fara ci, amma dai mutane sun yi mamakin yadda wutar ta yadu cikin sauri, yan kasuwa suk yi kokarin kwashe kayansu, amma wutar ta yi zafi.
"Muna kira ga gwamnati ta binciko abin da kw yawan jawo wannan gobara domin magance shi," In ji Aminu.

Gwamna Abba ya kai ziyara kasuwar Singa

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyara kasuwar Singer domin jajanta wa ‘yan kasuwar da gobara ta shafa.

Ya bayar da tabbatar masu da cewa gwamnatinsa za ta tsaya tsayin daka wajen tallafa masu da kula da su don rage radadin iftila'in da suka fada.

Gwamnan ya ba da umarnin gaggauta faɗaɗa da gyaran tituna a cikin kasuwar Singer domin sauƙaƙa zirga-zirga da kuma inganta harkokin kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262