Ramadan: Gwamnatin Jigawa Ta Fadi Tanadin da Ta Yi Wa Al'ummar Musulmi
- Gwamnatin jihar Jigawa ta shirya gudanar da shirin ciyarwa a lokacin azumin watan Ramadan na wannan shekarar hijira ta 1447
- Kwamishinan muhalli da canjin yanayi, Dr Nura Kazaure, ya bayyana cewa gwamnatin ya amince da kafa cibiyoyin ciyarwa kyauta
- Dr Nura Kazaure ya bayyana cewa za a rika ba da abincin buda baki ga al'ummar Musulmi a wadannan cibiyoyin da za a kafa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da kafa cibiyoyin ciyarwa kyauta guda 640 a faɗin jihar domin samar da abincin buɗa baki ga mutane miliyan 7.9 a lokacin watan Ramadan mai zuwa.
Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da Musulmin duniya ke shirin fara azumin Ramadan na kwanaki 29 ko 30 a ranar 17 ko 18 ga watan Fabrairun 2026.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Kwamishinan muhalli da canjin yanayi na jihar, Dr Nura Kazaure, ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan sakamakon taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a ranar Juma'a, 13 ga watan Fabrairun 2026.
Gwamnatin Jigawa za ta yi ciyarwa a azumi
Kwamishinan ya ce an ba da amincewar ne a yayin taron da Gwamna Umar Namadi ya jagoranta, shafin reubenabati.com.ng ya dauko labarin.
Nura Kazaure ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta shirya samar da abinci sama da miliyan 23.8 ga talakawa da gajiyayu a lokacin watan Ramadan.
"Ana sa ran shirin zai samar da kwanon abinci sama da 264,600 a kullum, inda adadin mutane daidai da haka za su amfana a kowace rana."
- Nura Kazaure
A ina za a rika ciyarwa a Jigawa?
Kwamishinan ya ƙara da cewa za a kafa waɗannan cibiyoyin ciyarwar ne a manyan makarantu, gidajen gyaran hali da kuma cibiyoyin jin daɗin jama'a, domin tabbatar da cewa shirin ya haɗa da kowa kuma ya isa ko'ina.
Kwamishinan ya bayyana cewa shirin yana da nufin samar da abinci mai gina jiki, tallafa wa gidajen da ba su da karfin tattalin arziki, da kuma karfafa dankon zumunci a tsakanin al'umma.
“Shirin yana da nufin samar da abinci mai inganci ga Musulmi masu azumi da sauran mazauna jihar masu buƙata, tallafa wa gidajen da ke da ƙaramin shiga da mutanen da ke fuskantar matsin tattalin arziki."
"Haɓaka haɗin kai, jinkai a tsakanin al'umma; sannan kuma ya zama ƙarin tallafi ga shirye-shiryen rage raɗaɗin fatara na gwamnatin jiha."
- Nura Kazaure

Source: Facebook
Gwamnati za ta sanya ido
Nura Kazaure ya ci gaba da cewa majalisar ta kuma ba da umarnin kiyaye inganci sosai wajen saye, sarrafawa, da kuma raba abincin, inda ya ƙara da cewa:
"Za a kafa kwamitocin sa ido a matakin jiha, kananan hukumomi, da mazabu domin tabbatar da an gudanar da aikin yadda ya kamata.”
A shekarun baya, an samu inda gwamnati ta koka da abincin da ake raba wa talakawa lokacin azumi.
Gwamna ya amince a biya albashi saboda azumi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya amince a biya ma'aikata albashin watan Fabrairun 2026.
Gwamna Ahmed Aliyu ya ce ya yi haka ne domin ma'aikatan jihar su fara azumin watan Ramadan cikin kwanciyar hankali.
Hakazalika, gwamnan ya yi kira ga ma’aikata da su mayar da martani ga wannan karamci ta hanyar kara himma, rikon gaskiya da jajircewa a aikinsu.
Asali: Legit.ng


