Amurka da Kwankwaso: Ndume Ya Yi Mamaki, Ya Nemi Tona Asirin Barayin Kasa
- Mohammed Ali Ndume ya yi magana game da zargin da wasu 'yan majalisar Amurka suka yi wa jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
- 'Yan majalisar sun yi zargi Sanata Rabiu Kwankwaso da tauye hakkin addini ga Kiristoci da neman a hana shi bizar shiga kasar baki daya
- A martanin da Sanata Ali Ndume ya yi, ya ce akwai abin mamaki a ce an ambaci sunan Kwankwaso duk da yadda aka san salon mulkinsa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Mohammed Ali Ndume ya yi magana kan yadda wasu 'yan majalisar Amurka ke neman kakaba takunkumi kan tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso.
Sanata Ali Ndume da ya fito daga jihar Borno ya yi magana yana mai bayyana lamarin a matsayin abin mamaki matuka kuma maras dacewa kwata-kwata.

Kara karanta wannan
Zargin Amurka: NNPP ta jingine siyasa, ta tura bukata ga Shugaba Tinubu kan Kwankwaso

Source: Facebook
Amurka: Maganar Ndume kan Kwankwaso
Legit Hausa ta gano cewa Sanata Ndume da ke wakiltar Borno ta Kudu ya yi magana kan Rabiu Kwankwaso ne yayin wata hira a shirin Politics Today a tashar Channels TV.
“Ina mamakin yadda aka ambaci sunan Kwankwaso, kuma ina son sanin dalili da yadda aka kawo sunansa cikin lamarin,”
Inji Sanata Ndume a shirin da aka watsa ranar Juma’a, 13 ga Fabrairun 2026.

Source: Facebook
Ndume ya kara da cewa:
“An ambaci Kwankwaso kaɗai, tsohon gwamna, lallai akwai lauje cikin nadi. Wataƙila akwai bayanan sirri da wasu suka sani amma wasu daga cikinmu ba mu sani ba.
“Ba na son zurfafawa cikin batun, amma a ganina, rike kadarori da takunkumin da Birtaniya, Amurka da sauran ƙasashe ke shirin kakabawa bai dace ba,”
In ji shi
A makon da ya wuce wasu ‘yan majalisar Amurka sun gabatar da wani kudirin doka, suna neman kakaba takunkumi kan Kwankwaso, ƙungiyar Miyetti Allah, da Miyetti Allah Kautal bisa zargin take ‘yancin addini.
Bukatar Ndume ga kasashen duniya
Sanata Ali Ndume ya buƙaci Amurka da sauran ƙasashe su daina batun sanya Najeriya a matsayin kasar da ke da ke bukatar kulawa ta musamman.
Vanguard ta rahoto ya ce:
“Idan suna son taimaka mana, ya kamata su mai da hankali kan ‘mutanen da ke da ’ maimakon yi wa ƙasa baki ɗaya wani lakabi da ‘Ƙasar mai bukatar kulawa,’”
Ndume ya bukaci kasashen waje su fallasa wadanda suka kai dukiyar Najeriya suka boye a ketare:
“Yawancin ‘yan Najeriya mutane ne marasa laifi. Amma akwai wasu kaɗan da suka tara kadarorin Najeriya a waje, kuma su (ƙasashen waje) sun san su, amma har yanzu ba a fallasa su ba.”
'Yan Kwankwasiyya sun kare Kwankwaso
A wani labarin, kun ji cewa Kungiyar Kwankwasiyya da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ke jagoranta ta yi watsi da kudirin wasu 'yan majalisar Amurka.
Ta ce saka sunan tsohon ministan tsaron Najeriyan cikin kudirin ba shi da tushe kuma “na siyasa ne, tana mai neman a cire sunansa nan take daga kudirin.
Kungiyar ta ce bayyana cewa waɗannan zarge-zarge ba su da wata alaƙa da abin da ke a fili a tarihin rayuwa da hidimar Sanata Kwankwaso.
Asali: Legit.ng
