Bayan Sha da Kyar, El Rufai Ya Fadi Adadin Jami'an Tsaron da Suka So Cafke Shi
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ba da bayanai kan yunkurin da jami'an tsaro suka yi na cafke shi a filin jirgin sama
- El-Rufai ya bayyana cewa an girke jami'an tsaro a filin jirgin saman domin cafke shi yana shigowa cikin Najeriya
- Ya bayyana cewa jami'an DSS aka turo domin su cafke shi, amma ya ki yarda ya bi su saboda ba su ba shi takarda ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi karin haske kan yunkurin da jami'an tsaro suka yi na cafke shi.
Nasir El-Rufai ya bayyana cewa jami’an tsaro na farin kaya (DSS) ne, ba na hukumar EFCC ba, suka yi yunƙurin kama shi ranar Alhamis a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja sa’ilin da ya dawo daga birnin Cairo na kasar Masar.

Source: Twitter
El-Rufai ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da tashar Arise News a ranar Juma'a, 13 ga watan Fabrairun 2026.
Wace hukuma ta so cafke El-Rufai?
Tsohon gwamnan na Kaduna ya yi ikirarin cewa hukumar ICPC ce ta jagoranci yunkurin cafke shi
El-Rufai ya bayar da labarin yadda gomman jami’an tsaro suka yi ƙoƙarin tsare shi da ƙarfin tsiya ba tare da wata takardar gayyata ta hukuma ba.
“Ina fitowa daga jirgi, sai wani saurayi sanye da rigar kwat ya ce shi daga DSS yake kuma yana so na bi shi zuwa ofishinsu. Na tambaye shi, ‘Ina takardar gayyatar take?’"
"Ya ce manyansa na da ita kuma zai raka ni zuwa gare su. Na gaya masa cewa dole ne na bi ta wajen jami’an shige da fice tukunna, kawai dai ka kawo mini takardar."
- Nasir El-Rufai
A cewarsa, karin jami’an tsaro sun bayyana sa’ilin da yake ƙoƙarin ƙarasa wa wajen tantance fasfo.
“Ashe sun tura kusan jami’an DSS 50 zuwa filin jirgin tare da takamaiman umarni na cewa a tsare ni, a yi garkuwa da ni, sannan a tsare ni."
- Nasir El-Rufai
El-Rufai ya ki yarda a tafi da shi
Ya kara da cewa wasu jami’ai biyu sun yi ƙoƙarin tura shi ta wata hanyar daban da karfi.
“Suka ce dole ne mu je ofishinsu. Na ce ba zan je ko’ina ba. Idan ba ku da takarda, ba zan bi ku ba. Ko shugaban ƙasa ba zai iya gaya mini cewa dole ne na yi wani abu ba. Wannan ƙasa ce mai ’yanci da dimokuradiyya."
- Nasir El-Rufai
Tsohon gwamnan ya jaddada cewa rahotannin farko da suka alaƙanta hukumar EFCC da wannan lamari ba daidai ba ne.
“Lauyoyina sun ambaci EFCC, amma ina so na bayyana ƙarara cewa, ba EFCC ba ne. DSS ne. ICPC ce ta dauko DSS domin su yi garkuwa da ni."
- Nasir El-Rufai

Source: Twitter
El-Rufai zai amsa gayyatar EFCC
Ya kara da cewa hukumar EFCC ta riga ta aika masa da takardar gayyata domin tattaunawa, kuma ya riga ya ba da amsa ta hannun lauyoyinsa.
“EFCC sun rubuto mini wasiƙa lokacin da nake kasar waje suna cewa suna so mu gana. Lauyoyina sun ba su amsa cewa ina hutu na shekara-shekara, kuma da zarar na dawo zan sanar da su."
"Zan yi bikin murnar zagayowar ranar haihuwata, sannan na zo na gan ku da ƙarfe 10:00 na safe ranar 16 ga watan Fabrairu.”
- Nasir El-Rufai
ICPC ta gayyaci El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Nasir El-Rufai, ya tabbatar da cewa zai amsa gayyatar da hukumar ICPC ta yi masa a ranar Laraba, 18 ga Fabrairun 2026.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa zai gabatar da kansa a ofishin hukumar kamar yadda aka tsara domin amsa dukkan tambayoyin da ake masa.
Asali: Legit.ng


