Kotu Ta Umarci a Kawo Malamin Musulunci da Ake Zargi da Hannu a Shirin Yiwa Tinubu Juyin Mulki
- Babbar kotun tarayya ta sake yin zama a yau Juma'a kan Sheikh Sani Abdulkadir Zaria da ake zargi da hannu a shirin juyin mulki a Najeriya
- A zaman wanda ya gudana a Abuja, Mai shari’a Peter Lifu ya umarci hukumar DIA ta gurfajar da Sheikh Sani Zaria a ranar 18 ga watan Fabrairu, 2026
- Alkalin ya bayyana cewa Najeriya na cikin yarjejeniyoyi daban-daban na kare hakkin dan adam, don haka ya kamata a yi wa malamin adalci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Leken Asirin Soji (DIA) ta gabatar da malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Abdulkadir Zaria, a gabanta.
Kotun ta umarci hukumar DIA ta gurfanar da Malamin, wanda ake zargi da hannu a wani shirin juyin mulki da aka yi wa Shugaba Bola Tinubu, a ranar 18 ga Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan
Lamari ya juya: Ƴan bindiga sun yi saɗaf saɗaf sun hallaka 'DPO' bayan sace shanu

Source: Facebook
Mai shari’a Peter Lifu ne ya bayar da umarnin a ranar yau Juma’a, 13 ga watan Fabrairu, 2026, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
Alkalin ya bayyana cewa dukkan hukumomi tsaron da ke tuhumar Sheikh Sani Zaria suna ƙarƙashin ikon farar hula, tunda ƙasar na ƙarƙashin mulkin dimokuraɗiyya.
Alƙalin ya ce dokokin da ke kunshe Sashe na 36 (1), (5) da (6) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 sun tanadi hakkin shari’a ga dukkan ‘yan ƙasa.
Ya kuma jaddada cewa Najeriya ta kulla yarjejeniyoyi daban-daban na ƙasa da ƙasa kan haƙƙin ɗan Adam, don haka ba za ta iya yin sakaci a irin waɗannan batutuwa ba.
Bukatar da lauyan Sheikh Sani Zariga ya shigar
Umarnin kotun ya biyo bayan korafin neman kare haƙƙin ɗan Adam da lauyoyin Sheikh Zaria, Sanusi Musa (SAN), Abdul Aliyu (SAN) da Mohammed Sheriff, suka shigar, suna ƙalubalantar tsare shi ba tare da gurfanar da shi a kotu ba

Kara karanta wannan
An gano matsalar da za a iya samu a zaben shugaban kasar 2027 saboda azumin Ramadan
An shigar da korafin ne kan Hukumar EFCC, DIA, Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, da kuma Jaiz Bank Plc, suna neman a sako malamin ya koma cikin iyalansa.

Source: Getty Images
Majiyoyi daga iyalansa sun danganta matsalar da malamin ya shiga da wata kyautar Naira miliyan 2 da aka tura asusun bankin wani jagoran ƙungiyar Fityanul Islam da ake tsare da shi, wanda aka ambata a cikin zargin shirin juyin mulki.
Kotu ta bukaci a bi doka a shari'ar Malam Sani
Alƙalin ya lura cewa tun ranar 11 ga Disamba, 2025, aka kama malamin ba tare da ba shi damar ganin iyalansa ko abokansa ba, bayan da aka fara bincike a kansa.
Kotun ta ce dole ne a bi doka da tanade-tanaden kundin tsarin mulki wajen kula da duk wanda ake zargi, komai nauyin zargin da ake yi masa, kamar yadda
Kotu ta nemi takardu daga DIA
A wani rahoton, kun ji cewa bangaren gwannatin tarayya ya gaza gabatar da takardun izinin kotu kan ci gaba da tsare malamin muslunci, Sheikh Sani Abdulkadir Zaria.
Jami'an tsaro na tsare da Sheikh Sani Abdulkadir Zaria, da ake zargi da hannu a shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Kotu ta nemi Hukumar Leken Asirin Soji (DIA) da ta gabatar da umarnin kotu da aka ce an samu kan tsare malamin ba tare da gurfanar da shi ba.
Asali: Legit.ng