Sharudan da ake Zargi Rasha Ta Sa kafin Daukar 'Yan Najeriya Soja

Sharudan da ake Zargi Rasha Ta Sa kafin Daukar 'Yan Najeriya Soja

  • Hukumar leken asirin sojin Ukraine ta ce ta gano wasu ‘yan Najeriya biyu da suka mutu a fagen daga yayin da ake zargin suna fafatawa a gefen Rasha
  • An bayyana sunayen ‘yan Najeriyar da Hamzat Kolawole da Mbah Udoka duk da cewa ba a yi karin bayani game da wasu abubuwa game da su ba
  • Kasar Kuraine ta wallafa wasu hotuna dauke da bayanan da ta ce su ne irin yarjejeniyar da Rasha ta kulla da matasan kafin daukarsu aikin soja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Ukraine - Kasar Ukraine ta fitar da sanarwar da ta nuna wasu 'yan Najeriya biyu da ta ce sun shiga aikin soja a Rasha kuma sun rasu a fagen daga.

A sanarwar da Ukraine ta fitar, ta ce Kazeem Kolawole ya shiga sojan Rasha a ranar 29 ga Agusta 2025, sannan Mbah Udoka kuma a ranar 28 ga Satumba.

Kara karanta wannan

INEC ta fadi dalilan sa zaben 2027 a Ramadan da matakin da za ta dauka

Wani dan Najeriya da ake zargi ya mutu a Rasha
Takardar da ake zargi ta kunshi yarjejeniyar Rasha da 'yan Najeriya. Hoto: Головне управління розвідки Міністерства оборони України
Source: Getty Images

Sanarwar da sojojin Ukraine suka wallafa a shafinsu na Facebook ta kunshi sharudan aiki da ta yi zargin 'yan Najeriyan sun kulla da Rasha.

Daukar 'yan Najeriya zuwa Rasha

Takardu biyu daga cikin uku da Ukraine ta wallafa kan zargin yarjejeniyar an rubuta su ne da harshen Rasha, yayin da ta uku ta ƙunshi harshen Rasha da Turanci.

Takarda ta uku da aka wallafa, wadda aka rubuta wani ɓangare da Turanci, tana kama da takardar kwantiragi da Kolawole ya sanya wa hannu.

Yan Najeriya da suka mutu Rasha
Kazeem Kolawole da Mbah Udoka da aka ce sun mutu a Rasha. Hoto: Головне управління розвідки Міністерства оборони України
Source: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa takardar ta ƙunshi sunansa, ranar haihuwarsa (23 ga Afrilu, 1983), da lambar fasfo dinsa В02437053.

Ƙarin bayani kan yarjejeniyar Rasha

A cewar takardar, kwantiragin yana aiki ne na tsawon shekara guda kawai, ta kuma nuna cewa bayan sanya hannu, za a tura Kolawole zuwa “rundunar soji masu kai farmaki.”

“Kwangilar da Ma’aikatar Tsaro za a kulla ta na tsawon shekara guda. Za a tura ku zuwa rundunar masu kai farmaki.

Kara karanta wannan

Yadda Ukraine ta kashe 'yan Najeriya da suka shiga sojan Rasha a fagen daga

“Idan kuna da wata niyya ta daban ta zuwa Rasha, ko kuka ƙi rattaba hannu kan kwantiragin, za a kai ku sashen ‘yan sanda, sannan ku jira watanni da dama a tsare kafin a mayar da ku ƙasarku, kuma za a haramta muku shiga Tarayyar Rasha har abada.
Haka kuma za ku biya kuɗin tikitin tafiya da dawowa,”

Inji takardar.

Legit Hausa bata tantance ingancin takardun da Ukraine ta fitar ba, kuma har zuwa lokacin hada wannan rahoton Rasha bata fito ta yi magana kan lamarin ba.

Wani dan Najeriya da aka ce ya mutu a Rasha
Dan Kano da aka ce ya mutu yana yaki a Rasha. Hoto: Anas Adam|Jafar Jafar
Source: Facebook

Dan Najeriya ya rasu cikin sojin Amurka

A wani labarin, kun ji cewa wani dan Najeriya mai shekara 21 da ya shiga rundunar sojin Amurka ya rasu a wani hadari da ya rutsa dashi.

Rahotanni sun nuna cewa sojan ya fado daga cikin wani jirgin ruwa ne ana tsaka da tafiya a cikin teku kuma an neme shi ba a gan shi ba.

Rundunar sojin Amurka ta tabbatar da rasuwarsa tare da karin bayani game da yadda aka nemi gawarsa, ta kuma tura sakon ta'aziyya ga iyalansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng