'Yan Ta'adda Sun Sace 'Dan Majalisar Dokokin Kaduna? An Fadi Abin da Ya Faru

'Yan Ta'adda Sun Sace 'Dan Majalisar Dokokin Kaduna? An Fadi Abin da Ya Faru

  • An yada wani rahoto mai ikirarin cewa 'yan ta'adda sun yi garkuwa da dan majalisar da ke wakiltar mazabar Kajuru a majalisar dokokin jihar Kaduna
  • Majalisar dokokin jihar ta fito ta musanta inda ta bayyana halin da dan majalisar yake ciki bayan yada rahoton sace shi
  • Ta yi gargadi ga kafafen yada labaran da ke yada abubuwa ba tare da tantancewa ba, tare da yin barazanar daukar matakin shari'a

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Majalisar dokokin jihar Kaduna ta yi martani kan rahoton da ke cewa 'yan ta'adda sun yi garkuwa da daya daga cikin mambobinta.

Majalisar ta bayyana rahoton da ke ikirarin sace dan majalisa mai wakiltar mazabar Kajuru, Hon. Usman Stingo, a matsayin karya.

Majalisar dokokin Kaduna ta musanta batun sace mambanta
Ginin majalisar dokokin jihar Kaduna Hoto: Kaduna State House of Assembly
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce shugaban kwamitin yaɗa labarai, kungiyoyi masu zaman kansu na majalisar, Marah Henry, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis, 12 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

IFAD: Ministan Tinubu ya samu gagarumar nasara, an ba shi babban mukami a duniya

Me majalisa ta ce kan sace mambanta?

Marah Henry ya ce rahoton da wata kafar yaɗa labarai ta intanet ta wallafa na kanzon kurege ne kuma tatsuniya ce kawai, jaridar Theeagleonline ta kawo rahoton.

Henry ya ce ɗan majalisar mai wakiltar Kajuru yana cikin ƙoshin lafiya kuma a halin yanzu yana gudanar da ayyukansa.

Ya ƙara da cewa mutumin da aka ambata a cikin rahoton an yi kuskuren siffanta shi ne a matsayin mamba na majalisar dokokin jihar Kaduna.

A cewarsa, hoton da aka yi amfani da shi a rahoton ba na dan majalisar ba ne, wanda hakan ke nuna rashin kyakkyawan bincike daga ɓangaren mawallafin.

“Rahoton karya ne gaba ɗayansa kuma ƙirƙirarren abu ne kawai a cikin tunanin mawallafin."
“Wani yunƙuri ne da aka tsara domin dasa tsoro, haifar da hargitsi a tsakanin jama’a, da kuma rage kwarin gwiwar jama’a kan karfin jami’an tsaron gwamnati."

- Henry Marah

Majalisar dokokin Kaduna ta yi gargadi

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun yi hayaniya, an buga muhawara a kan aika sakamakon zabe

Henry ya gargaɗi kafafen yaɗa labarai kan yaɗa bayanan da ba a tantance ba, yana mai cewa majalisar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen neman hakkinta a gaban shari’a ga kowane mutum ko hukuma da aka samu da laifin yaɗa bayanan ɓata suna.

Majalisar dokokin Kaduna ta ce ba a sace mambanta ba
Taswirar jihar Kaduna, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya jaddada cewa yayin da aka amince da ’yancin ’yan jarida a cikin kundin tsarin mulki, bai kamata a yi amfani da shi wajen inganta aikin jarida wanda zai iya yin barazana ga zaman lafiyar jama’a da tsaro ba.

Shugaban kwamitin ya bukaci jama’a da su yi watsi da rahoton kuma su kwantar da hankulansu, tare da ba da tabbacin cewa gwamnatin jiha tana ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyi.

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci a wani kauye da ke karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benue.

​Yan bindigan sun kashe ’yan sanda biyu da fararen hula hudu yayin wani harin da suka kai a kauyen Tse-Kaseve da ke gundumar Anyagba.

Majiyoyi sun bayyana cewa ’yan bindigan dauke da makamai sun mamaye yankin ne a kan babura kusan 100.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng