Ramadan na Karatowa, za a Yi Gyaran Iskar Gas da zai Rage Wutar Lantarki a Najeriya

Ramadan na Karatowa, za a Yi Gyaran Iskar Gas da zai Rage Wutar Lantarki a Najeriya

  • An fara gargadin cewa tashoshin wutar Najeriya bakwai za su fuskanci ƙarancin iskar gas yayin gyara da za a yi watan Fabarairun 2026
  • Ana hasashen cewa za a samu gibin samar da wutar lantarki da kusan kashi 19.67 a Najeriya saboda gyare-gyaren da za a yi
  • Hukumar NISO mai kula da wutar lantarki a Najeriya ta bayyana muhimman matakan da za a dauka a kwanakin da za a shafe ana gyaran

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Fargabar ɗaukewar wuta a sassa daban-daban na Najeriya na ƙaruwa bayan kamfanin Seplat ya rufe wata babbar cibiyar samar da iskar gas domin gyara.

Hukumar NISO ta yi gargaɗin cewa tashoshin wuta bakwai a faɗin ƙasar za su fuskanci karancin iskar gas, lamarin da ka iya haifar da ƙarancin wutar lantarki a tushen wuta na kasa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sa kayan sojoji, sun sace mata a gidan biki a Kano

Wani waje da ya shafi lantarki a Najeriya
Wasu ma'aikatan TCN a bakin aikin wutar lantarki. Hoto: Transmission Company of Nigeria
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto cewa NISO ta ce aikin gyaran da aka tsara daga 12 zuwa 15 ga Fabarairu, 2026, zai rage yawan iskar gas da ake bai wa wasu tashoshin wuta.

Tashoshin wutar da abin zai shafa

Tashoshin wutar da ake sa ran za su fi fuskantar tasiri kai tsaye sun haɗa da Egbin, Azura, Sapele da Transcorp, yayin da NDPHC Sapele, Olorunsogo da Omotosho za su iya fuskantar matsala 'yar kadan.

A cewar NISO, gyaran zai shafi iskar gas da ke shiga hanyar bututun NNPC NGIC, lamarin da ake sa ran zai rage ƙarfin samar da wutar lantarki na ɗan lokaci a kan tushen wuta na ƙasa.

Gibin wutar lantarki da za a samu

Wata sanarwa ta dabam da kakakin NNPCL, Andy Odeh, ya fitar ta tabbatar da cewa za a rage iskar gas ga tashoshin wuta bakwai da ke kan tushen lantarki na ƙasa a tsawon kwanaki huɗu na aikin.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Tinubu na shirin sayar da manyan kadarorin Najeriya

Rahotanni daga NISO sun nuna cewa aikin gyaran na iya haifar da gibin samar da wuta da ya kai megawatt 934.96, wanda ya kai kusan kashi 19.67.

Rahoton da jaridar Vanguard ta fitar ta nuna cewa sanarwar ta ce za a dawo da iskar gas kamar yadda ya ke a baya a ranar 16 ga Fabarairu, 2026.

Ranar da za a kammala gyaran tana dab da fara azumin watan Ramadan na 2026, wanda idan aka samu matsala ba a kammala ba za a iya jefa jama'a a karin wahala.

Ministan makamashin Najeriya
Ministan makamashi na kasa a wani taro. Hoto: Adebayo Adelabu
Source: Facebook

Matakan da za a ɗauka kan lantarki

Rahotanni sun nuna cewa NISO ta bayyana cewa za ta ɗauki matakai domin tabbatar da daidaito a lokacin gyaran da za a yi.

Ta ce idan ya zama dole a rage lodin wuta, za a yi hakan cikin tsari, gaskiya da adalci tare da haɗin gwiwa da kamfanonin rarraba wuta.

Ma'aikatan KEDCO sun yi yajin aiki

A wani labarin, kun ji cewa ma'aikatan wutar lantarki karkashin kamfanin rarraba wuta na KEDCO sun shiga yajin aiki a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi jihohin Arewa 2 da za a tura dakarun sojoji na musamman

A bayanin da suka fitar, ma'aikatan sun bayyana cewa sun dauki matakin ne saboda rike musu wasu hakkokinsu da hana su karin girma.

Sai dai kamfanin KEDCO ya karyata zargin yana mai cewa yana bin matakan da suka dace wajen karin girma ba tare da nuna wariya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng