'Abin da Tinubu Zai Yi kan Tura Sakamakon Zabe Ta Hanyar Yanar Gizo'

'Abin da Tinubu Zai Yi kan Tura Sakamakon Zabe Ta Hanyar Yanar Gizo'

  • Ana ci gaba da muhawara a Najeriya kan batun tura sakamakon zabe kai tsaye ta yanar gizo da majalisar dattawa ta amince da shi
  • Hadimin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa babu kasar da take aiki da tsarin sadarwa wanda bai da matsala
  • Sunday Dare ya bayyana cewa Shugaba Tinubu zai dauki matakin da ya dace dangane da batun tura sakamakon zabe ta yanar gizo

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan kafafan yada labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya yi magana kan batun tura sakamakon zabe ta yanar gizo.

Sunday Dare ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai dauki mataki cikin tsanaki game da tura sakamakon zabe ta hanyar yanar gizo, tare da la’akari da yanayin gaskiya da ake ciki a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun yi hayaniya, an buga muhawara a kan aika sakamakon zabe

Shugaba Tinubu zai yi matsaya kan tura sakamakon zabe ta yanar gizo
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Hadimin na shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayim wata tattaunawa da ya yi da tashar Arise News, a ranar Alhamis, 11 ga watan Fabrairun 2026.

An amince da tura sakamakon zabe ta intanet

Kwanan nan ne majalisar dattawa ta amince da kudirin kwaskwarima ga dokar zabe, inda ta yarda da tura sakamakon zabe ta yanar daga rumfunan zabe zuwa rumbun adana bayanan sakamako na INEC wata (IReV).

Majalisar ta bayar da damar cewa za a iya yin amfani da tura sakamako ta hanyar rubutawa a takarda idan aka samu matsalar rashin yanar gizo a wurin.

Wannan amincewa ta biyo bayan kwanaki ana zanga-zanga daga kungiyoyin farar hula wadanda suka bukaci majalisar dattawa ta wajabta tura sakamakon zabe kai-tsaye ta yanar gizo daga rumfunan zabe.

Wane mataki Shugaba Tinubu zai dauka?

Yayin da yake jawabi a hirar, Sunday Dare ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa shugaban kasar, wanda ya siffanta shi da cikakken dan kishin dimokuradiyya, zai yi abin da ya fi dacewa ga kasar.

Kara karanta wannan

Dokar zabe: Majalisar Dattawa ta sauya matsaya kan tura sakamako ta yanar gizo

“Ina tabbatar muku cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, sanannen dan kishin dimokuradiyya ne, kuma zai yi abin da yake daidai, amma hakan ba zai kasance ba tare da duba yanayin gaskiya na kasarmu ba."

- Sunday Dare

Sbugaba Tinubu zai dauki mataki kan tura sakamako ta yanar gizo
Mai girma Bola Ahmed Tinubu, shugaban kasar Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Hadimin Tinubu ya nuna shakku

Yayin da yake nuna shakku kan yiwuwar tura sakamako 100% kai-tsaye, Sunday Dare ya kafa hujjar cewa babu kasar da take da tsarin sadarwa da yake aiki ba tare da kuskure ba.

“Babu inda ake tura sakamako 100% kai-tsaye. Shin kuna gaya mini cewa wannan kasar, kamar yadda take a yanzu, tana da yanar gizon da ya isa a ce za a gudanar da tsarin turawa 100%?”

- Sunday Dare

Tinubu ya nada sabon shugaban NAHCON

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON).

Shugaba Bola Tinubu ya nada Ismail Abba Yusuf a matsayin wanda zai jagoranci hukumar NAHCON bayan murabus din Farfesa Abdullahi Sale Usman.

Rahotanni sun nuna cewa sabon shugaban na NAHCON ya rike mukamin Jakadan na musamman na Najeriya a Türkiyya daga shekarar 2021 zuwa 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng