Malaman Musulunci Sun Bambanta kan Yi wa Sarkin Musulmi Biyayya a Ramadan

Malaman Musulunci Sun Bambanta kan Yi wa Sarkin Musulmi Biyayya a Ramadan

  • Kungiyar MUSWEN da manyan malaman Musulmi sun jaddada bin umarnin Sarkin Musulmi kan fara azumin Ramadan
  • Sun gargadi Musulmi da su guji duk wata sanarwa ta kashin kai kan ganin wata, suna cewa hakan na iya haddasa rarrabuwar kawuna
  • Hakan ya biyo bayan sanar da ranar fara azumin Ramadan da wasu malaman yankin suka yi ba tare a duba girman Sarkin Musulmi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Yayin da watan Ramadan ke karatowa, Kungiyar Al’ummar Musulmi ta Kudu maso Yammacin Najeriya (MUSWEN) sun nuna suna tare da Sarkin Musulmi.

Musulman tare da manyan shugabannin Musulmi a yankin sun sake jaddada aniyarsu ta gudanar da azumin bana karkashin jagorancin Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar.

Shugabannin Musulmi sun nuna goyon baya ga Sarkin Musulmi a Ramadan
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Mohammad Sa'ad Abubakar III. Hoto: The Sultanate Media Team.
Source: Facebook

Ramadan: Limaman Musulunci sun hada kai

MUSWEN tare da Babban Limamin Daular Oyo, Sheikh Bilal Husayn Akinola Akeugberu; Babban Limamin Lagos, Sheikh Sulaimon Oluwatoyin Abou Nolla, Sheikh Dhikrullahi Shafi’i, sun bayyana cewa babu wanda ya isa ya ayyana fara Ramadan da kansa, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Yunkurin juyin mulki: Kotu ta fusata game da ci gaba da tsare malamin Musulunci

Kungiyar ta sake nuna cikakken goyon bayanta ga jagorancin Sarkin Musulmi a matsayinsa na Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA).

A cikin wata sanarwa da shugaban MUSWEN, Alhaji Rasaki Oladejo, da Sakatare, Farfesa Wole Abbas, suka sanya wa hannu, an ce wata sanarwar da aka yi kan fara azumin Ramadan na 2026 sun sabawa tsarin da aka amince da shi na ganin wata.

Sanarwar ta ce an yi wadannan shela ne ba tare da la’akari da tsarin da NSCIA ke bi karkashin jagorancin Sarkin Musulmi ba wajen tabbatar da fara azumi.

Kungiyar ta yi kira ga Musulmi a Kudu maso Yamma da ma kasa baki daya da su guji rarrabuwar kawuna, tana mai gargadin su da su kula da masu kokarin haddasa rabuwar kai da sunan addini.

Ta ce:

“Manufarsu ita ce raba kan Musulmi domin su ci galaba a kansu. Kada mu fada tarkonsu.”
An samu mabambantan ra'ayoyi kan biyayya ga Sarkin Musulmi a Ramadan
Sarkin Musulmin Najeriya, Mai Alfarma Muhammad Sa'ad Abubakar III. oto: National Moon Sighting Committee.
Source: Facebook

Ramadan: Waye Musulman Oyo za su bi?

A nasa bangaren, Sheikh Akeugberu ya tabbatar da cewa Musulmin Oyo za su bi jagorancin Sarkin Musulmi a dukkan lamurran addini, yana mai cewa hakan ya dace da koyarwar Alkur’ani da Hadisi.

Kara karanta wannan

Matsalolin da za a iya fuskanta hajjin bana bayan Sheikh Pakistan ya y murabus

Ya kuma bayyana cewa ba za a ayyana fara azumin Ramadan a Oyo ba sai an saurari sanarwar hukuma daga Sarkin Musulmi, cewar Muslims News Nigeria.

Haka zalika, Sheikh Abou Nolla ya bayyana cewa Musulmin Jihar Lagos za su jira sanarwar ganin watan Ramadan daga Sarkin Musulmi kafin su fara azumi.

A wani sakon bidiyo, ya bukaci Musulmi su kasance masu hakuri da hadin kai, yana mai cewa bin jagorancin Sarkin Musulmi wajibi ne kuma hanya ce ta tabbatar da daidaito.

Shi ma Sheikh Dhikrullahi Shafi’i ya jaddada cewa babu wanda ke da ikon ayyana fara azumi shi kadai, domin wannan hakki na shugabannin da aka amince da su ne a Musulunci.

Saudiyya ta magantu kan duba watan Ramadan

Mun ba ku labarin cewa kasar Saudiyya ta bukaci musulmi da su fara duba jinjirin watan Ramadan a yammacin ranar Talata, 17 ga watan Fabrairu, 2026.

Idan har an ga watan a ranar Talata, to za a fara azumin Ramadan ranar Laraba, 18 ga watan Fabrairu, kamar yadda sanarwa ta nuna.

Har ila yau, idan kuma ba a ga watan ba, to watan Sha'aban zai cika kwanaki 30, sannan a fara azumin Ramadan a ranar Alhamis, 19 ga watan na Fabrairun 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.