Kashim Shettima Ya Fice daga Najeriya, Zai Wakilci Tinubu a Muhimmin Taro
- Jirgin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya tashi daga babban birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis, 12 ga watan Fabrairun 2026
- Kashim Shettima ya tashi daga birnin Abuja ne domin zuwa kasar Ethiopia halartar taron kungiyar Tarayyar Afrika (AU)
- Mataimakin shugaban kasar zai gudanar da tarurruka da manyan shugabannin kasashe a yayin ziyarar ta sa a kasar Ethiopia
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya tashi daga Abuja zuwa birnin Addis Ababa na kasar Habasha (Ethiopia).
Kashim Shettima ya je kasar ne domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron kungiyar Tarayyar Afirka (AU) na shekarar 2026.

Source: Twitter
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan kafafan yada labarai da sadarwa (ofishin mataimakin shugaban kasa), Stanley Nkwocha, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 12 ga watan Fabrairun 2026 a shafin X.
An yi wa taron taken “tabbatar da dorewar samun ruwa da ingantattun tsarin tsaftar muhalli domin cimma burukan ajandar 2063,”
Taron zai mayar da hankali ne kan ciyar da alkawuran nahiyar gaba wajen dorewar sarrafa ruwa, inganta tsarin tsaftar muhalli, da kuma manyan muradun ci gaba da ke kunshe a cikin tsarin ajandar 2063 na kungiyar AU.
Shettima zai halarci tarurruka
Sanarwar ta Stanley Nkwocha ta kara da cewa yayin da yake Addis Ababa, mataimakin shugaban kasar zai kasance tare da sauran shugabannin Afirka a zama na 39 na taron shugabannin kasashe da na gwamnatocin kungiyar AU.
Kashim Shettima zai kuma kasance tare da shugabanni a babban taron majalisar karo na 30, wadanda aka tsara gudanarwa a ranakun 14 da 15 ga watan Fabrairu, 2026.
Haka kuma, a gefen taron, Shettima zai halarci wasu manyan tarukan da za a gudanar da tattaunawa da shugabannin siyasa da na kasuwanci.
Za a gudanar da tarurrukan ne da nufin karfafa dangantakar diflomasiyya, tattalin arziki, da dabarun hadin gwiwa na Najeriya a fadin nahiyar.
Yaushe Shettima zai dawo
Mataimakin shugaban kasar ya samu rakiyar ministoci da sauran manyan jami'an gwamnati.
Ana sa ran zai dawo Najeriya bayan kammala ayyukansa na hukuma a birnin Addis Ababa.

Source: Twitter
Karanta wasu labaran kan Kashim Shettima
- Zaben 2027: An ba Shugaba Tinubu mafita kan yadda zai yi da Kashim Shettima
- Abin da Shugaba Tinubu ya ce kan Shettima yayin da ake jita jitar sauya shi a 2027
- Shettima ya bude sabon shirin tallafa wa matasa miliyan 10 a harkar kudi
Tinubu ya tura Shettima zuwa Kwara
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura Kashim Shettima zuwa jihar Kwara bayan harin da 'yan ta'adda suka kai.
Kashim Shettima ya je jihar Kwara ne domin jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar bisa mummunan harin da aka kai a ƙauyen Woro da ke ƙaramar hukumar Kaiama.
Ziyarar na da nufin nuna goyon bayan gwamnatin tarayya ga al’ummar da abin ya rutsa da su, tare da jajanta musu kan mummunan lamarin da ya girgiza jihar.
Asali: Legit.ng

