Hedkwatar Tsaro Ta Jero Abubuwan da Sojojin Amurka 200 Za Su Yi idan Suka Shigo Najeriya
- Hedkwatar tsaron kasa ta fito ta yi bayani yayin da aka fara nuna fargaba kan shirin Amurka na turo karin sojoji 200 zuwa Najeriya
- Mai magana da yawun hedkwatar tsaro, Manjo Janar Samaila Uba ya ce sojojin Najeriya ne za su ci gaba da jagorantar kowane aiki
- Ya ce sojojin Amurka za su taimaka ne a fannin horar da jami'ai, tattara bayanan sirri da sauran harkokin fasahar zamani a yaki da ta'addanci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ana ta tambayoyi da nuna damuwa bayan rahoton cewa Amurka za ta turo karin sojoji 200 zuwa Najeriya.
Masu ruwa da tsaki da dama na nuna fargabar cewa matakin na iya zama wata hanya ta kafa sansanin sojin Amurka a ƙasar.

Source: Facebook
Abubuwan da sojojin Amurka za su yi
Jami’an Najeriya da na Amurka sun ce sojojin za su taimaka ne wajen horas da dakarun Najeriya a yaƙin da suke yi da ƙungiyoyin jihadi, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Mai magana da yawun Hedikwatar Tsaro ta Najeriya, Manjo Janar Samaila Uba, ya tabbatar da shirin turo sojojin Amurka 200 Najeriya, inda ya ce:
“Za mu karɓi sojojin Amurka domin su taimaka mana a bangaren horo da tallafin fasaha.”
Ya kuma tabbatar wa Reuters cewa sojojin Amurka ba za su shiga faɗa da yan ta'adda kai tsaye ba.
“Ba za su yi aikin yaƙi kai tsaye ba, kuma ba za su jagoranci ayyukan soji ba. Dakarun sojojin Najeriya ne za su ci gaba da riƙe cikakken iko da yanke duk wata shawarar aiki a kan ƙasar su,” in ji Uba.
Yaushe sojojin Amurka za su iso Najeriya?
Ya ƙi bayyana ranar da za su iso, amma ya ce matakin na cikin haɗin gwiwar da ake yi tsakanin Najeriya da Amurka ƙarƙashin Kwamitin Haɗin Gwiwa na Ƙasashen biyu.
An ruwaito cewa sojojin za su ƙara wa wata ƙaramar tawagar Amurka da ke taimaka wa Najeriya wajen tsara hare-haren sama.
Ana sa ran karin sojojin za su iso cikin makonni masu zuwa, domin su ba da horon aiki da shawarwarin fasaha, musamman wajen daidaita hare-haren sama da na ƙasa a lokaci guda.
Amurka ta taso Najeriya kan matsalar tsaro
A ‘yan kwanakin nan, Najeriya na fuskantar matsin lamba daga Amurka kan matsalar tsaro. Shugaban Amurka, Donald Trump, ya taba bayyana lamarin a matsayin mai tsanani da kuma kisan Kiristoci.
Gwamnatin Najeriya ta sha musanta zargin cewa ana muzguna wa Kiristoci a hukumance, tana mai cewa matsalar tsaro ta shafi kowa.

Source: Getty Images
Duk da ana ganin turo karin sojoji 200 na nuna ƙara zurfafa haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Najeriya, hedkwatar tsaro ta jaddada cewa:
“Sojojin Amurka ba za su shiga yaƙi kai tsaye ko gudanar da ayyukan soja ba.”
Sojojin Amurka sun ziyarci Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi wata babbar tawagar sojojin Amurka a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Tawagar ta Amurka ta zo ƙarƙashin jagorancin Kwamandan Rundunar Sojojin Amurka a Afirka (USAFRICOM), Janar Dagvin R. Anderson, tare da wasu jami’ai.
Sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar ta ce Shugaba Tinubu ya tarbi Janar Dagvin Anderson tare da babban jami'i a ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, Keith Heffern.
Asali: Legit.ng

