Kwankwaso: NNPP Ta Yi Martani Mai Zafi da Amurka Ta Kawo Batun Kakaba wa Jagoranta Takunkumi
- Wasu 'yan majalisar dokokin Amurka sun gabatar da kudiri wanda idan aka amince da shi zai sanya a sakawa Rabiu Musa Kwankwaso, takunkumi
- Jam'iyyar NNPP ta fito ta yi martani bayan da aka nemi saka Kwankwaso cikin wadanda ake zargi da take hakkin 'yancin addini da matsa wa kiristoci
- NNPP ta bayyana dalilin da ya sa 'yan majalisar kasar Amurkan ke neman saka tsohon gwamnan na Kano cikin zargin muzgunawa Kiristoci a Najeriya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar NNPP ta yi martani kan wani kudiri da aka gabatar a gaban majalisar dokokin Amurka, wanda zai shafi Rabiu Musa Kwankwaso.
Jam'iyyar NNPP ta yi Allah wadai da kudirin wanda ke neman sanya wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, takunkumi bisa zargin take hakkin 'yancin bin addini.

Source: Facebook
Jaridar TheCable ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na NNPP, Ladipo Johnson, ya fitar ranar Laraba, 11 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan
Babu sauki: Sojoji sun yi raga raga da 'yan ta'addan ISWAP, an kashe tsageru da dama
Jam'iyyar NNPP ta kare Rabiu Kwankwaso
Ladipo Johnson, ya yi watsi da zargin, inda ya siffanta matakin a matsayin “shirin da aka kulla” domin bata sunan mutumin da ba shi da laifi kuma ba shi da wata alaka da tsattsauran ra’ayin addini.
“Muna kallon wannan lamari a matsayin wata kullalliya da aka yi wa mutumin da ba shi da laifi, wanda a fili yake cewa ba shi da wata alaka da tsattsauran ra’ayin addini a Najeriya.”
“Tarihinsa yana nan a fili ga kowa, ko dai lokacin da yake riƙe da mukamin gwamnati ko kuma a rayuwarsa ta kashin kai. Yana da kyau mutane su binciki irin wadannan abubuwa yadda ya kamata kafin su yanke hukunci.”
- Ladipo Johnson
Meyasa Amurka ta huro wa Kwankwaso wuta
Ladipo Johnson ya bayyana cewa wannan mataki ya samo asali ne sakamakon martanin da Kwankwaso ya yi kan matakin Shugaban Amurka Donald Trump na sake sanya Najeriya a cikin jerin “kasashe masu matsala ta musamman"

Kara karanta wannan
'Dan Majalisar wakilai daga Kano na tsaka mai wuya, NNPP na neman raba shi da mukaminsa
Riley Moore, wanda shi ne ya gabatar da kudirin, ya tambayi Kwankwaso a bainar jama’a game da “rawar da ya taka a kisan Kiristoci,” inda ya kafa hujja da kaddamar da cikakken tsarin shari’ar Musulunci a jihar Kano lokacin da Kwankwaso yake gwamna.
Amma Ladipo Johnson ya soki dan majalisar na Amurka kan matsayar da ya dauka kan Kwankwaso, inda ya nuna cewa jagoran na NNPP ya kasance mai yawan magana kan rashin tsaro a kasar kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
Jam'iyyar NNPP ta jefo tambayoyi
“Shin Riley Moore yana yin adalci ne ko kuwa zabar abin da yake so yake yi? Shin Amurka ba ta da kyakkyawar alaka da Qatar da Saudiyya (wadanda duka kasashe ne masu bin tafarkin shari’a)?”
“Shin ba abin mamaki ba ne cewa Kwankwaso, wanda yake jagoran 'yan adawa ya yi magana sau da dama game da rashin tsaro a karkashin wannan gwamnati, shi ne Amurka take neman tasowa a gana a yanzu?”
- Ladipo Johnson
Ya kuma kara da cewa lokacin da yake gwamnan Kano, Kwankwaso ya kawar da Boko Haram daga jihar kuma yana da kyakkyawar alaka da shugabannin Kiristoci.
Matar Ganduje ta ba Kwankwaso shawara

Kara karanta wannan
'Tinubu ya fara yi wa godiya, ba Allah ba': Naja'atu Mohammed ta dura kan Abba Kabir
A wani labarin kuma, kun ji cewa uwargidan tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Hajiya Hafsat Abdullahi Ganduje, ta ba Rabiu Musa Kwankwaso shawara.
Hafsat Ganduje ta ce ya kamata Kwankwaso ya bar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gudanar da mulkinsa cikin kwanciyar hankali domin amfanin al’ummar jihar Kano.
A cewarta, lokaci ya yi da tsohon gwamnan na Kano zai nuna girma ta hanyar yafiya da goyon bayan ci gaban jihar fiye da rike sabanin siyasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng