Abin da Gwamnatin Najeriya Ta Yi da Aka Tuntube Ta kan Kudirin Majalisar Amurka
- An nemi jin ta bakin gwamnatin Najeriya bayan yan Majalisar Amurka sun gabatar da wani kudiri da nufin magance zargin kisan kiristoci
- Ministan Yada Labarai da wayar da kai, Mohammed Idris ya ki yarda ya ce komai kan wannan batu, wanda ya fara jan hankalin mutane
- Kungiyoyi da shugabannin addini sun sha kira ga gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen dakile tashin hankalin da ke shafar Kiristoci da Musulmi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya ta kama bakinta kan kudirin doka da yan Majalisar dokokin Amurka suka gabatar da nufin magance zargin kisan kiristoci a Najeriya.
Da aka tuntube shi ranar Laraba, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Mohammed Idris, ya ƙi yin tsokaci kan kudirin ‘yan majalisar Amurka.

Source: Facebook
Yadda aka tuntubi gwamnatin tarayya
Vanguard ta tuntubi Gwamnatin Tarayya don ta yi martani kan yunkurin majalisar Amurka tare da fadin matakan da take ɗauka domin shawo kan matsalolin da ke da nasaba da addini ba tare da matsin lambar ƙasashen waje ba.
Shirun da ministan ya yi na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen waje ke ci gaba da sanya ido kan matsalolin tsaro da kuma rikice-rikicen da ke da nasaba da addini a wasu sassan Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa kudirin dokar da ake tattaunawa a majalisar dokokin Amurka na da nufin ƙarfafa sa ido kan yanayin ‘yancin addini a Najeriya.
Najeriya ta dage kan musanta zargin
A lokuta da dama, Najeriya ta sha nanata cewa matsalolin tsaronta suna da sarkakiya kuma ba wai addini kaɗai ne tushensu ba, kamar yadda tashar Channels tv ta ruwaito.
Gwamnatin ta ce yawancin hare-hare na da alaƙa da ta’addanci, fashi da makami, rikice-rikicen ƙabilanci da sauran laifuffuka, ba wai wani addini kadai aka tauye ba.
Masu sa ido kan al’amura sun bayyana cewa shirun da ministan ya yi na nuna yadda batun yake da matuƙar mahimmanci, musamman ganin yadda Najeriya ke kula da dangantakarta ta diflomasiyya da Amurka da sauran ƙasashe.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Bayan turo sojoji, an hango abin da Amurka za ta yi a zaben Najeriya na 2027

Source: Getty Images
Kungiyoyin fararen hula da shugabannin addini sun sha kira ga gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen dakile tashin hankalin da ke shafar Kiristoci da Musulmi, musamman a yankin Arewa ta Tsakiya da wasu sassan Arewa maso Gabas.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, Ma’aikatar Yaɗa Labarai ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba domin bayyana matsayar Gwamnatin Tarayya kan kudirin dokar na Amurka.
Amurka za ta kara turo sojoji 200 Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa Amurka ta shirya turo sojoji akalla 200 zuwa Najeriya domin horas da sojojin kasar kan yaki da ‘yan ta’adda a yankuna daban-daban.
Wannan na zuwa ne bayan shugaba Donald Trump ya bayar da umarnin kai hare-hare a wuraren da ya bayyana a matsayin sansanonin kungiyar ISIS a Najeriya.
Rahoto ya nuna cewa sojojin Amurka 200 da za a turo za su kara karfi ne ga wasu jami’an sojin kasar da tuni suke Najeriya domin taimaka wa dakarun cikin gida.
Asali: Legit.ng
