Hankali Ya Tashi: NSIB Ya Fitar da Jawabi da Jirgi Ya Samu Matsala a Sararin Samaniya

Hankali Ya Tashi: NSIB Ya Fitar da Jawabi da Jirgi Ya Samu Matsala a Sararin Samaniya

  • Jirgin saman kamfanin Arik Air ya yi saukar gaggawa a Benin City bayan samun matsalar inji yayin da yake kan hanyar zuwa Fatakwal
  • An ce masana kanikanci za su tantance jirgin samfurin Boeing kafin ya koma aiki domin tabbatar da tsaro da kiyaye rayukan fasinjoji
  • Hukumar da ke binciken hadurra ta Najeriya (NSIB) ta fitar da sanarwa game da halin da fasinjoji 80 da ma'aikatan jirgin suke ciki yanzu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benin - Fasinjojin jirgin Arik Air dake kan hanyar su ta zuwa Fatakwal daga Legas sun shiga fargaba yayin da jirgin ya karkata zuwa birnin Benin.

Matuƙan jirgin sun yanke shawarar yin saukar gaggawa ne bayan sun ji wani ƙara mai ƙarfi daga injin hagu na jirgin samfurin Boeing 737-700 a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Jirgi ya samu matsala a sama bayan dauko 'yan Najeriya kusan 100

Jirgin sama dauke da fasinjoji 80 ya samu matsalar inji a hanyar zuwa Fatakwal
Jirgin sama mallakin kamfanin Arik Air a yana tafiya a sararin samaniya. Hoto: Arik Air
Source: Facebook

Jirgi ya samu matsala a samaniya

Hukumar kamfanin ta tabbatar da cewa jirgin mai lamba 5N-MJF ya sauka lafiya a filin jirgin Benin ba tare da samun wani ƙarin matsala ba, in ji rahoton Daily Trust.

Dukkan fasinjoji 80 da ma'aikatan jirgin sun sauka lafiya, inda kamfanin ya nemi afuwar su tare da samar da dabarun kankama su zuwa Fatakwal.

Hukumar NSIB ta fitar da sanarwa a shafinta na X, inda ta tabbatar da cewa injin jirgin na Arik ya samu matsala, wanda ya tilasta shi saukar gaggawa.

Sanarwar ta ce:

"Hukumar binciken hadurra ta Najeriya (NSIB) ta tabbatar da cewa jirgin kamfanin Arik kirar B737-7GL (5N-MJF) da ke sufuri tsakanin Legas da Fatakwal ya gamu da matsalar inji, kuma an karkatar da shi zuwa Benin.
"Jirgin ya sauka lafiya. Dukkan fasinjoji da ma'aikatan jirgin na cikin koshin lafiya. Za a samar da karin bayanai nan gaba."

Kara karanta wannan

Hafsun sojoji ya fadi abin da ke jiran wadanda suka kitsa juyin mulki

Karanta sanarwar a nan kasa:

Wasu matakai da aka dauka

Manajan yaɗa labarai na kamfanin Arik Air, Adebanji Ola, ya jaddada cewa kiyaye rayukan fasinjoji shine babban burin kamfanin su a kowane lokaci.

"Kare lafiyar fasinjoji shi ne babban burinmu a Arik Air. Muna matukar ba da hakuri ga fasinjojin Fatakwal da wannan abu ya faru da su, lallai an kawo tsaiko ga tafiyarsu."

- Adebanji Ola.

Rahoto ya nuna cewa masana injiniyancin jiragen sama za su gudanar da cikakken bincike kan jirgin kafin a ba shi damar ci gaba da gudanar da zirga-zirga a ƙasar.

Jirgin saman Arik Air ya samu matsalar inji a sararin samaniya dauke da fasinjoji 80
Yadda injin jirgin saman Arik Air ya lalace a hanyarsa ta zuwa Fatakwal daga Legas. Hoto: @aviationbrk
Source: Twitter

Hotunan lalacewar jirgin saman

Tuni dai aka ce kamfanin ya yi wasu shirye shirye na sufurin fasinjojin da abin ya shafa zuwa Fatakwal, inda can ne dama aka je kai su.

Wasu hotuna da shafin 'Breaking Aviation News' ya wallafa a shafinsa na X, sun nuna yadda injin jirgin na Arik Air ya faffashe.

Kalli hotunan a kasa:

Wani jirgi ya yi hatsari a jihar Imo

Kara karanta wannan

Karshen duniya: Ta kwabe wa yaro bayan zargin shi da hannu a garkuwa da mahaifinsa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani karamin jirgin sama kirar Cessna 172 ya gamu da hatsari a filin jirgin Owerri bayan ya samu matsala a sararin samaniya.

Jirgin da ya taso daga Kaduna zuwa Port Harcourt dauke da manyan mutane ya yi kokarin sauka a Owerri saboda matsalar da ya samu, amma ya yi hatsari.

Yayin da aka fara bincike, hukumar NSIB ta ce gobara ba ta tashi ba bayan hatsarin, sannan ta bayyana halin da mutane hudu da ke a jirgin suke ciki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com