Bayan Murabus Din Pakistan, an Gano yadda Shettima Ya Sauya Tunanin Saudiyya
- Saudiyya ta kara wa Najeriya lokaci domin kammala shigar da bayanan maniyyata aikin Hajjin 2026 a dandalin Nusuk Masar
- Karin lokacin ya zo ne bayan sa hannun gwamnatin tarayya, bisa umarnin Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima
- Hukumar NAHCON ta gargadi masu shirya Hajji da su yi gaggawa, domin wannan karin lokaci na kwanaki ne kacal
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Maniyyatan Najeriya da ke shirin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 sun samu sassauci daga kasar Saudiyya.
Hakan ya biyo bayan da aka kara wa Najeriya wa’adin shigar da bayanan maniyyata a dandalin Nusuk Masar.

Source: Facebook
Maniyyata sun sake samun dama a hajjin 2026
Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta yanke wannan hukunci, bayan sa hannun gwamnatin tarayyar Najeriya, domin bai wa maniyyatan da ba su kammala shigar da bayanansu ba damar yin hakan, cewar Tribune.
Tun da farko, wa’adin shigar da bayanan maniyyata na Hajjin bana ya kare ne a ranar Lahadi, 8 ga watan Fabrairu, kuma Saudiyya ta jaddada cewa ba za a kara lokaci ba.
Sai dai a ranar Litinin, Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar da ‘yan Najeriya cewa an rufe dandalin, tare da gargadin kada a biya kudin Hajji ga kowanne mutum ko hukuma.
A wata sabuwar sanarwa da ta fitar daga baya, NAHCON ta bayyana cewa hukumomin Saudiyya sun amince da karin lokaci na musamman ga Najeriya, bayan shiga tsakani da gwamnatin tarayya ta yi.

Source: Facebook
Gargadin da Saudiyya ta yi ga hukumomin Najeriya
Mataimakiyar Daraktar Yada Labarai da Hulda da Jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta ce bisa umarnin Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tugga, ya tuntubi hukumomin Saudiyya domin neman wannan sassauci.
Ta ce Saudiyya ta amince da bukatar, amma ta jaddada cewa bayan karewar wannan karin lokaci, ba za a sake amincewa da wani roko ba.
Usara ta bukaci dukkan masu kula da aikin Hajji a Najeriya da su yi aiki dare da rana domin kammala shigar da bayanan maniyyata cikin gaggawa.

Kara karanta wannan
Hajji: Matsala ta tunkaro wasu maniyyatan Najeriya, NAHCON ta roki Saudiyya alfarma
Ko da yake ba a bayyana tsawon karin lokacin a hukumance ba, rahotanni sun nuna cewa Saudiyya ta ba Najeriya kwanaki bakwai kacal domin kammala shigar da bayanan maniyyata da rarrabasu a dandalin Nusuk Masar.
NAHCON ta kuma ja hankalin hukumomin Hajji da su guji jinkiri, domin kauce wa matsaloli a kafin fara aikin Hajjin 2026, cewar Punch.
Wannan na zuwa ne kwana daya bayan tsohon shugaban hukumar, Sheikh Abdullahi Saleh Usman Pakistan ya yi murabus daga mukaminsa a kashin kansa.
'Dalilin da ya sa na yi murabus' - Sheikh Pakistan
Mun ba ku rahoton cewa Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya fadi dalilin yin murabus daga mukamin Shugaban hukumar alhazai ta NAHCON.
Sheikh Abdullahi Pakistan ya ce ya ajiye aikin ne bayan addu’a da tuntubar iyalansa, tare da jaddada cewa bai da wata matsala da gwamnati.
Tsohon shugaban NAHCON ya gode wa Bola Tinubu, Kashim Shettima da sauran masu ruwa da tsaki a kasa da kuma hukumar.
Asali: Legit.ng
