Karshen Duniya: Ta Kwabe wa Yaro bayan Zargin Hannu a Garkuwa da Mahaifinsa
- Rundunar ‘yan sanda a Adamawa ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da garkuwa da Alhaji Ahmadu a karamar hukumar Fufore
- Abin mamaki, daya daga cikin wadanda aka kama shi ne ɗa ne ga wanda aka sace a jihar wanda ya ba al'umma mamaki
- ‘Yan sanda sun ce ana ci gaba da kokarin ceto wanda aka sace lafiya tare da farautar sauran mambobin kungiyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yola, Adamawa – Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa ta yi nasarar cafke wasu matasa uku kan zargin garkuwa da mutane.
An cafke mutane ne kan zargin hannu a garkuwa da Alhaji Ahmadu a yankin Malabu da ke karamar hukumar Fufore.

Source: UGC
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafin Facebook.
Yan sanda sun kama barayin mutane 3
Nguroje ya ce an kama su ne bayan wani samame na musamman bisa sahihan bayanan sirri, tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na cikin al’umma.
A cewar sanarwar, rundunar ta samu gagarumar nasara a yaki da garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka, sakamakon tsare-tsaren sirri da aka aiwatar tare da masu ruwa da tsaki na tsaro a yankin.
An ce samamen ya biyo bayan sace Alhaji Ahmadu da aka yi a ranar 30 ga Janairu, 2026, a Malabu.
Sanarwar ta kara da cewa, bisa umarnin Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Dankombo Morris, rundunar tare da mambobin Miyetti-Allah sun kai samame maboyar masu garkuwa da mutane da ke kauyen Jera a gundumar Malabu.
‘Yan sandan sun fadi sunayen wadanda aka kama da Lawali Haruna mai shekaru 45, Yahaya Ibrahim mai shekaru 25, da kuma Da’u Alhaji Ahmadu mai shekaru 28.

Source: Original
Abin mamaki ya faru bayan cafke mutanen
Abin da ya kara tada hankali shi ne yadda aka gano cewa daya daga cikin wadanda ake zargin ɗa ne ga Alhaji Ahmadu da aka sace.
Sanarwar ta ce:
“Abin damuwa shi ne, daya daga cikin wadanda ake zargin shi ne ɗa ne ga wanda aka sace, duk mutanen ukun sun amsa laifin hannu a cikin wannan aika-aika.”
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa ana ci gaba da kokarin ceto Alhaji Ahmadu cikin koshin lafiya tare da kama sauran mambobin kungiyar masu laifi.
Kwamishinan ‘yan sandan ya yaba da hadin gwiwar da aka samu tsakanin ‘yan sanda da jami’an tsaro na cikin al’umma, yana mai jaddada kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyi.
Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai a kan lokaci, yana mai cewa za a sanar da jama’a duk wani sabon bayani yayin da bincike ke ci gaba.
An kara yawan yan sanda a Adamawa
A baya, an ji cewa rundunar ‘yan sandan Adamawa ta tura ƙarin jami’ai bayan gwamnati ta kafa takunkumin fita na sa’o’i 24 a Lamurde.
An umarci mazauna yankunan da su zauna a gidajensu don kauce wa ƙarin rikici da tabarbarewar tsaro da ya addabi yankin.
Harin da ake zargin mayakan ƙabilu daga Gombe ne suka kai ya yi sanadin mutuwa da lalata kauyuka da dama duk da batun sulhu.
Asali: Legit.ng


