Ana Maganar Dokar Zabe, ’Yan Majalisa Sun Kaure da Fada a Zamansu a Abuja
- An samu cacar baki mai zafi a Majalisar Tarayya yayin kare kasafin kudin Ma’aikatar Noma ta 2026 kan rashin bayani da gaskiya
- Dan majalisa Awaji-Inombek Abiante ya zargi shugabanni da kokarin toshe muhawara kan kasafin kudi mai cike da matsala
- Ma’aikatar Noma ta ce kalubalen hauhawar kayan aiki da jinkirin sakin kudade na barazana ga tsaron abinci a Najeriya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – An samu rikici da cacar baki yayin zaman kare kasafin kudin shekarar 2026 na Ma’aikatar Noma da Tsaron Abinci ta Tarayya a Majalisar Tarayya.
Rikicin ya barke ne a zaman hadin gwiwa tsakanin kwamitocin Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai kan Noma, Ayyuka da Raya Karkara.

Source: Twitter
Dalilin fadan yan majalisar dokoki a Najeriya
Rahoton Premium Times ya ce lamarin ya faru ne lokacin da Karamin Ministan Noma da Tsaron Abinci, Sabi Abdullahi, ya gabatar da kasafin kudin ma’aikatar.
Dan Majalisar Wakilai daga Jihar Rivers, Awaji-Inombek Abiante (APC), ya kalubalanci kasafin, yana cewa babu isasshen bayani, tsari da kuma adalci a cikin shirye-shiryen da aka gabatar.
Abiante ya tambayi ko kasafin ya bi ka’idojin da suka dace yana mai cewa yawancin abubuwan da ke ciki ba su da cikakken bayani da zai tabbatar da gaskiya da rikon amana.
Yayin da yake kokarin yin karin bayani, Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai, Bello Ka’oje (APC, Kebbi), ya bugi kararrawa domin dakatar da shi, amma Abiante ya ki barin magana.
Ya ce an zabe shi ne domin kare muradun jama’arsa, ba wai muradin shugabancin kwamitin ba, yana zargin shugabannin da kokarin rufe baki da hana sahihiyar muhawara.
A cewarsa, rashin tilasta bayani da gaskiya a kasafin na iya rushe duk tsarin kasafin kudin kasar nan baki daya.

Source: Twitter
Martanin ministan noma a Najeriya
A nasa bangaren, Ministan Noma, Sabi Abdullahi ya kare kasafin, yana cewa an gina shi ne bisa dokar gaggawar tsaron abinci da Shugaba Bola Tinubu ya ayyana, sakamakon hauhawar farashi da karancin abinci.

Kara karanta wannan
Akwai kura: Dan majalisa ya tsallake rijiya da baya bayan fusatattun matasa sun farmake shi
Ministan ya bayyana cewa duk da karuwar samar da noma, har yanzu ana fuskantar manyan kalubale kamar tsadar taki, kayan aiki da jinkirin fitar da kudade.
Ya ce a kasafin 2026, ana sa ran bangaren noma zai samu kusan Naira tiriliyan daya, yayin da Ma’aikatar Noma za ta samu kimanin Naira biliyan 262 na ayyukan ci gaba da biliyan 19.18 na kudin gudanarwa.
Sanatoci da ‘yan majalisa sun nuna damuwa cewa rage kasafin noma na iya kara tabarbarewar tsaron abinci, cewar The Nation.
Majalisa ta yi watsi da kasafin kudin sojoji
An ji cewa majalisar tarayyar Najeriya ta yi watsi da kasafin kudin rundunar sojojin sama na shekarar 2026 da muke ciki.
Shugaban kwamitin, Sanata Osita Ngwu ya ce kudin da aka ware wa rundunar ya yi kadan kwarai wajen yaki da 'yan ta'adda a kasar.
An kafa kwamitin mutum shida don tattaunawa da gwamnatin tarayya domin samar da kasafin kudin da zai wadaci ayyukan rundunar.
Asali: Legit.ng
