Magana Ta Fito: Sheikh Pakistan Ya Fadi Dalilin Murabus daga Shugabancin NAHCON

Magana Ta Fito: Sheikh Pakistan Ya Fadi Dalilin Murabus daga Shugabancin NAHCON

  • A karshe, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya yi murabus daga mukamin Shugaban NAHCON, lamarin da ya ba mutane mamaki
  • Sheikh Abdullahi Pakistan ya fadi dalilin yanke shawarar bayan addu’a da tuntubar iyalansa, tare da jaddada cewa bai da wata matsala da gwamnati
  • Tsohon shugaban NAHCON ya gode wa Bola Tinubu, Kashim Shettima da sauran masu ruwa da tsaki a kasa da kuma hukumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - A wani lamari da ya ja hankalin al’ummar Musulmi a Najeriya, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya yi murabus daga mukamin Shugaban hukumar AHCON.

Sheikh Abdullahi Pakistan ya ajiye mukaminsa ne daga ranar Litinin 9 ga Fabrairu, 2026 bayan fuskantar zarge-zarge.

Sheikh Pakistan ya fadi dalilin ajiye muƙamin shugaban NAHCON
Shugaban hukumar alhazai ta NAHCON. Sheikh Usman Saleh Pakistan. Hoto: NAHCON.
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da ya fitar da Vanguard ta gano, Farfesa Usman ya bayyana cewa murabus ɗin ya kasance na kashin kansa, ba tare da wani matsin lamba ba.

Kara karanta wannan

Abin da Shugaba Tinubu ya ce kan Shettima yayin da ake jita jitar sauya shi a 2027

Ya ce bayan yin addu’a da kuma tuntubar iyalansa, ya yanke shawarar cikin kyakkyawar niyya da cikakken girmama nauyin aikin gwamnati.

Godiyar da Sheikh Pakistan ya yi wa Tinubu

Farfesan ya mika takardar murabus dinsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda Sashe na 3(6) na Dokar Kafa Hukumar NAHCON ta shekarar 2006 ta tanada.

Ya nuna godiya matuƙa ga Shugaba Tinubu bisa amincewa da girmamawar da ya ba shi na yi wa ƙasa da al’ummar Musulmi hidima.

Haka kuma, ya yaba wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, yana cewa shawarwari da goyon bayansa sun kasance masu muhimmanci ƙwarai a lokacin mulkinsa.

Farfesa Pakistan ya gode wa mambobin kwamitin NAHCON, ma’aikata da abokan hulɗa, ciki har da hukumomin jihohi da kamfanonin aikin Hajji, cewar Premium Times.

Ya ce haɗin kai da waɗannan bangarori, gami da hukumomin Saudiyya, ya taimaka sosai wajen inganta gudanar da aikin Hajjin Najeriya.

Sheikh Pakistan ya yi godiya ga Tinubu, Kashim
Tsohon shugaban hukumar NAHCON, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan. Hoto: NAHCON.
Source: Facebook

Dalilin murabus na Sheikh Abdullahi Pakistan

Tsohon shugaban NAHCON ya jaddada cewa murabus ɗinsa bai da alaƙa da rashin gamsuwa da hukumar ko gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi zai hada kai da Iran, ya fadi harkokin da za su yi tare

Ya ce shawarar ta samo asali ne daga dalilai na kashin kai kawai, kuma ba ta nuna wata matsala da manufar aikin Hajji ba.

A ƙarshe, Farfesa Usman ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da ba NAHCON nasara, tare da roƙon Allah ya ba alhazan gaba ikon yin karbabbiyar ibada.

Hukumar NAHCON ta bayyana cewa ayyukanta za su ci gaba da tafiya yadda ya kamata yayin da ake jiran sanar da sabon shugaba kafin Hajjin 2026.

Harajin da maniyyata za su biya

Kun ji cewa rahoto ya nuna Gwamnatin tarayya na shirin samun biliyoyin Naira daga alhazan Najeriya na Hajjin 2026 ta hanyar kudin hidima na 2%.

Kungiyar Independent Hajj Reporters (IHR) ta ce kowane maniyyaci zai biya kimanin N136,417, wanda za a tura kai tsaye zuwa Babban Bankin Najeriya.

Ta bukaci gwamnati da CBN su bayyana yadda ake amfani da kudin, tare da rokon Majalisar Tarayya ta yi bincike kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.