Dokar Zabe: Majalisa Ta Sauya Matsaya kan Tura Sakamako Ta Yanar Gizo

Dokar Zabe: Majalisa Ta Sauya Matsaya kan Tura Sakamako Ta Yanar Gizo

  • Majalisar dattawan Najeriya ta yi zama don duba batutuwan da suka jawo cece-kuce kan gyaran da aka yi wa dokar zabe ta shekarar 2026
  • A yayin zaman majalisar an tattake waje kan tanadin da ke neman tilastawa hukumar INEC tura sakamakon zabe ta yanar gizo
  • Babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Mohammed Monguno, ya gabatar da kudirin neman a yi wa wani sashe na dokar kwaskwarima

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta sauya matsayarta kan kin amincewa da tanadin tura sakamakon zabe kai tsaye ta hanyar yanar gizo.

Majalisar dattawan ta janye matsayar da ta cimma a baya na kin amincewa da tura sakamakon zabe kai-tsaye daga rumfunan zabe zuwa shafin adana bayanan sakamako na hukumar INEC watau (IReV).

Majalisar dattawa ta amince da gyara a dokar zabe
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da sanatoci yayin zaman majalisa Hoto: @SenateNGR
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce majalisar dattawan ta cimma wannan matsayar ne yayin zamanta na ranar Talata, 10 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Dokar zabe: Rikici ya barke a zaman Majalisar Dattawa kan wasu kalaman Akpabio

Majalisa ta amince da tura sakamako ta yanar gizo

Wannan matsayar ta biyo bayan dubawa da amincewa da wani kudiri da babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Mohammed Monguno (APC, Borno ta Arewa) ya gabatar yayin zaman gaggawa na majalisar a Abuja.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Abba Moro, ne ya goyi bayan wannan kudiri, jaridar The Punch ta kawo labarin.

An yi gyara a sashe na 60(3) na kudurin dokar gyaran dokar zabe ta 2026 kafin majalisar ta amince da shi.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta sabon gyaran kafin ya saka batun a matsayin kuri'a.

“Sashen da ake muhawara a kansa ya tanadi cewa jami’an zabe za su tura sakamako ta yanar gizo daga rumfunan zabe zuwa shafin IReV na INEC, sannan muddin idan tura sakamakon ta yanar gizo ya faskara ko kuma ya yi wahala, to Fom din EC8A zai zama matakin farko na tattara sakamako.”

- Godswill Akpabio

Kara karanta wannan

Dokar zabe: Amaechi ya tafi da dansa wajen zanga zanga a majalisar dattawa, ya fadi dalili

Majalisar dattawa ta sauya matsaya

Sanata Mohammed Monguno ya bayyana cewa shawarar janye kin amincewar da majalisar ta yi a baya ya samo asali ne daga bukatar ganin cewa dokar zaben ta yi daidai da muradin 'yan Najeriya.

“Wannan gyara an yi shi ne domin dokokinmu su zama iri daya da ra’ayi da buri na al’umma."

- Sanata Mohammed Monguno

Majalisar dattawa ta sauya matsaya kan dokar zabe
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Mafi akasarin sanatocin sun kada kuri’ar amincewa da sabon gyaran lokacin da aka gabatar da batun domin kada kuri’a.

Tun da farko dai an yi hatsaniya a zaman majalisar dattawan yayin da sanatoci suka yi muhawara kan gyaran dokar zaben.

Amaechi ya shiga zanga-zanga kan dokar zabe

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya shiga cikin masu zanga-zangar neman amincewa da tanadin tura sakamakon zabe ta yanar gizo.

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya je majalisar tarayya ne domin gudanar da zanga-zangar tare da babban dansa.

Amaechi ya bayyana cewa ya bukaci dansa, wanda likita ne, da ya shiga zanga-zangar domin ya taimaka wa masu zanga-zangar da ke bukatar kulawar likita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng