Abin da Shugaba Tinubu Ya Ce kan Shettima yayin da Ake Jita Jitar Sauya Shi a 2027
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya halarci taron majalisar tattalin arziki ta kasa (NEC), da aka gudanar a birnin tarayya Abuja
- Mai girma Bola Tinubu ya yi wasu kalamai kan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, a wurin taron da aka gudanar
- Hakazalika, Shugaba Tinubu ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na kawar da matsalar rashin tsaron da ta addabi kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi magana mai muhimmanci kan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
Shugaba Tinubu ya bayyana mataimakin shugaban Kasa, Kashim Shettima, a matsayin “abokin tafiya na gari a tafiyar neman ci gaba.”

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake bude taron majalisar tattalin arziki ta kasa (NEC), a dakin taro na fadar shugaban kasa a ranar Litinin, 9 ga watan Fabrairun 2026.
Haka kuma, ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na murkushe ta’addanci da ayyukan 'yan bindiga, wadanda ya ce ba abubuwan da za a yarda da su ba ne kuma baki ne ga al’adu da dabi’un Najeriya.
Me Tinubu ya ce kan Shettima?
Yayin girmama manyan baki, ya bayyana Shettima a matsayin:
“Mai girma mataimakin shugaban kasa kuma shugaban majalisar tattalin arziki ta kasa, Kashim Shettima, abokin tafiya na gari a tafiyar neman ci gaba."
Kalaman shugaban kasar sun jawo tafi daga gwamnoni, ministoci, manyan jami’an gwamnati, da shugabannin kamfanoni masu zaman kansu da suka halarci taron.
Hadimin shugaban kasa, Dada Olusegun ya sanya bidiyon jawabin Shugaba Tinubu a shafinsa na X.
Tinubu na kokarin samar da tsaro
Yayin da ya koma kan jawabin nasa, Shugaba Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya sabon kokari na karfafa dakarun tsaro da maido da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.
Ya bayyana rashin tsaro a matsayin babban cikas ga tattalin arziki, sannan ya jaddada bukatar daukar matakin bai-daya domin magance shi.
Yayin da yake maraba da mahalarta taron na kwanaki biyu, shugaban kasar ya ce wannan taro ya nuna irin hadin kan da ake da shi wajen ganin kasar ta ci gaba.
Me Tinubu ya ce kan manufofin gwamnatinsa?
Da yake bayyana nasarorin gwamnatinsa, Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da ake gudanarwa sun taimaka wajen daidaita tattalin arzikin kasar da kuma maido da amincewar kasashen duniya.
Ya kara da cewa bunkasa ababen more rayuwa a fannonin sufuri, wutar lantarki, fasahar sadarwa, gidaje, da tsarin ban-ruwa suna nan a matsayin muhimman abubuwan da ya sa a gaba.

Source: Facebook
Sanata Kashim Shettima ya yi jawabi
A nasa jawabin, Shettima ya yi kira da a samar da hadin kai mai zurfi tsakanin matakan gwamnati guda uku, inda ya bayyana NEC a matsayin wani dandamali mai muhimmanci na tsara alkiblar tattalin arzikin Najeriya.
Ya bukaci mambobin da su ba da fifiko wajen rage radadin talauci, samar da ayyukan yi, da kuma dorewar tsarin kashe kudade na kasa.
Tinubu ya sasanta Wike da Fubara
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya sake shiga tsakani kan rikicin siyasar jihar Rivers.
Shugaba Bola Tinubu ya kira manyan 'yan siyasar biyu don warwarewa rikicin siyasar wanda ya ki ci ya ki cinyewa.
Majiyoyi sun bayyana cewa akwai alamun Wike da Fubara sun sasanta domin tare suka tafi a mota daya bayan kammala ganawa da Shugaba Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


