Tinubu Ya Kawo Sabuwar Dabarar Tsaro a Arewa Maimakon Hana Hako Ma'adanai

Tinubu Ya Kawo Sabuwar Dabarar Tsaro a Arewa Maimakon Hana Hako Ma'adanai

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba za ta dakatar da harkokin hakar ma’adanai a daukacin Arewa ba duk da kiraye-kirayen gwamnonin yankin
  • Ministan raya albarkatun ƙasa ya bayyana cewa daukar matakin zai jefa Arewa da ƙasa baki ɗaya cikin matsanancin koma bayan tattalin arziki
  • Maimakon haka, gwamnati ta ce tana aiwatar da dabarar tsaro ta musamman domin murkushe ‘yan ta’adda a yankunan da matsalar ta fi tsanani

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta bayyana matsayarta a kan matsalar tsaro da ke addabar wasu sassan Arewacin Najeriya, inda ta ce ba za ta amince da dakatar da dukkan harkokin hakar ma’adanai ba.

Matsayar ta biyo bayan kiraye-kirayen da aka yi na neman dakatar da hakar ma’adanai na tsawon wata shida, da nufin rage hanyoyin samun kudin da ‘yan bindiga ke samu.

Kara karanta wannan

Za a samu sauki, Tinubu ya amince a bude iyakar Najeriya da Nijar don kasuwanci

Wasu gwamnonin Arewa yayin taro a Kaduna
Gwanonin Arewa a wani taron da suka yi game da tsaro. Hoto: Isma'ila Uba Misilli
Source: Facebook

Punch ta rahoto gwamnatin ta ce bayan la’akari da batun tsaro da kuma tasirin tattalin arziki, ta fahimci cewa rufe dukkan wuraren hakar ma’adanai zai fi haifar da illa mai yawa.

Maganar haƙo ma'adanai a Arewa

Ministan raya albarkatun ƙasa, Dele Alake, ya bayyana cewa dakatar da hakar ma’adanai gaba ɗaya a Arewa ba abu mai yiwuwa ba ne, domin hakan zai kawo mummunan tasiri ga tattalin arzikin yankin da ƙasa baki ɗaya.

Ta bakin hadiminsa na yada labarai, Segun Tomori, ministan ya ce gwamnati ta auna barazanar tsaro da kuma muhimmancin ci gaba da hakar ma’adanai da sarrafa su a Arewa.

A cewarsa, akwai manyan masana’antu da dama da ke dogaro kai tsaye da ma’adanan Arewa, ciki har da cibiyoyin sarrafa lithium a Nasarawa da Abuja da kuma masana’antar sarrafa ƙarfe a jihar Kaduna.

Muhimmancin ma’adanai ga tattalin arziƙi

Ministan ya kuma bayyana cewa har masana’antar siminti da ke Ajaokuta a jihar Kogi na dogaro da farar ƙasa, wanda ke nuna cewa dakatar da hakar ma’adanai zai shafi sassa da dama na tattalin arzƙki.

Kara karanta wannan

Harin Kwara: Kungiyar CAN ta tura muhimmin sako ga Musulmi da aka hallaka

Saboda haka, gwamnatin tarayya ta jaddada cewa hukunta dukkan masu hakar ma’adanai na halal saboda masu hakar ba bisa ka’ida ba ba zai zama mafita ba.

Sabuwar dabarar tsaro a Arewa

Maimakon dakatarwa baki ɗaya, gwamnatin ta ce tana aiwatar da dabarar tsaro ta musamman wadda ke mayar da hankali kan yankunan da ‘yan bindiga ke amfani da hakar ma’adanai wajen samun kudi.

Dabara na gudana ne ta hanyar haɗin gwiwar hukumomi daban-daban, karkashin kulawar ofishin Mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, inda ake aiwatar da ayyuka a sassan Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.

Wani waje da ake hakar ma'adanai
Wani mai hakar ma'adanai a bakin aiki. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tun a watan Disamban 2025 jaridar Business Day ta rahoto cewa masu hako ma'adai sun gargadi gwamnatin tarayya kan amincewa da bukatar gwamnonin.

An kashe masu haƙar ma'adanai

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun kai farmaki kan wasu masu hakar ma'adanai a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a Filato.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai farmaki ne cikin dare, inda suka yi dirar mikiya suka kashe mutane babu gaira babu dalili.

Dakarun sojojin Najeriya sun kai dauki ga masu hakar ma'adanan kuma ta yi karin bayani kan asarar da 'yan ta'addan da suka jawo a wajen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng