'Yan Bindiga Sun Yi Kisa yayin da Suka Sace Limami, Ladan da Wasu Mutane

'Yan Bindiga Sun Yi Kisa yayin da Suka Sace Limami, Ladan da Wasu Mutane

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya
  • Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka wani mutum tare da sace wasu mutanen da suka fita neman abin sanyawa a bakin salati
  • Majiyoyi sun bayyama cewa daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su zuwa cikin daji har da wani limami da ladan dinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Wasu ’yan bindiga sun kai hari a yankin Dogon Ruwa da ke gundumar Bashar a karamar hukumar Wase ta jihar Plateau.

'Yan bindigan sun kashe wani mazaunin yankin guda daya, tare da yin garkuwa da wani limami, ladan dinsa, da wasu mutane shida.

'Yan bindiga sun sace Limami da wasu mutane a Plateau
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa lamarin ya auku ne a yammacin ranar Lahadi, 8 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe bayin Allah, sun sace babban malami da wasu mutane 10

Dogon Ruwa na daya daga cikin yankunan da ke fama da yawaitar hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane a baya-bayan nan.

'Yan bindiga sun kai hari a Plateau

Mazauna yankin sun bayyana cewa an kai wa mutanen hari ne a bayan gari yayin da suke tsaka da samar da gawayi don sayarwa, rahoton DailyPost ya tabbatar da hakan.

Wani shugaban matasa a Wase, Shapi’i Sambo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa harin ya jefa mazauna yankin cikin fargaba.

Yayin da yake ba da labarin yadda abin ya faru, Shapi'i Sambo ya ce:

“Wadanda aka kai wa harin na tsaka da harkar gawayi ne sa’ilin da ’yan bindigan suka bayyana ba zato ba tsammani. Malam Abdulrashid Baduku, wani limami na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), da ladan dinsa na daga cikin wadanda aka sace.”

Mutanen gari sun bi sawun 'yan bindiga

Ya kara da cewa bayan harin, mazauna yankin sun bi sawun maharan amma ba su yi nasarar cimma su ba saboda lokacin yamma ta yi.

Kara karanta wannan

Ana zargin yaran Turji sun yi ajalin liman da basarake, jama'a sun tarwatse

Shapi'i Sambo ya bayyana cewa an tura jami’an tsaro yankin, tare da karin wasu dakarun domin karfafa tsaro, inda ya bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Alabo Alfred, bai ba da amsar tambayoyin da aka yi masa ba kan harin.

'Yan bindiga na kai hare-hare a Plateau

Wannan ba shi ne karon farko da yankin na Dogon Ruwa ke fuskantar hare-hare ba daga wajen 'yan bindiga.

'Yan bindiga sun sace mutane a Plateau
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

A ranar, 29 ga Yuli, 2025 'yan bindiga sun yi wa sojoji da ’yan banga kwanton bauna a yankin, inda suka kashe sojoji biyu da ’yan banga biyu.

Hakazalika a ranar Litinin da ta gabata, 'yan bindiga sun kai hari garuruwan Sabon Gari da Zak, inda suka kashe mutane biyar da soja daya.

Tinubu ya damu kan ayyukan 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna matukar damuwarsa kan ayyukan 'yan bindiga.

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa 'yan bindiga da 'yan ta'adda na cutar da tattalin arzikin Najeriya ta hanyar yi masa illa.

Mai girma Bola Tinubu ya sha alwashin daukar matakan da suka dace domin murkushe 'yan bindiga da 'yan ta'adda a kasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng