Tsohon Gwamnan Bauchi Ya Bada Shawara a kan Binciken Gwamnatin Bala Mohammed
- Tsohon gwamnan Bauchi, Ahmed Adamu Mu’azu, ya gargadi sabuwar gwamnati kan ɓata lokaci da kuɗi wajen binciken Bala Mohammed
- Ahmed Adamu Mu'azu ya yabawa ayyukan more rayuwa da gwamnatin Sanata Bala Mohammed ta aiwatar a faɗin jihar daga 2019 zuwa yau
- Muazu wanda ya shiga ofis a 1999 ya bayyana cewa da zarar gwamnatin Bola Mohammed ta sauka, a mayar da hankali a kan aiki ga jama'a
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi – Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Ahmed Adamu Mu’azu, ya shawarci duk wata sabuwar gwamnati da za ta hau mulki bayan Gwamna Bala Mohammed.
Ahmed Adamu Mu’azu ya bayar da shawara a kan cewa kada sabuwar gwamnati ta ɓata lokacinta da albarkatunta wajen binciken gwamnatin Sanata Bala Abdulkadir Mohammed.

Source: Facebook
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa Ahmed Adamu Mu’azu, wanda ya mulki Bauchi daga 1999 zuwa 2007, ya bayyana hakan ne yayin wani taron lacca na cikar jihar shekaru 50 da kafuwa.
An gudanar da taron ne a dakin taro na Ahmadu Bello International Conference Centre da ke Bauchi.
An bayar da shawara kan gwamnan Bauchi
Independent Newspaper ta wallafa cewa Gwamna Bala Mohammed, wanda aka fara zaɓensa a 2019 sannan aka sake zaɓarsa a 2023, na dab da kammala wa’adinsa na biyu a shekara mai zuwa.
A cewar tsohon gwamnan, babu wani amfani a sake buɗe shafukan baya, musamman idan akwai abubuwa masu kyau da aka samar.
Ya shawarci sabuwar gwamnati da ta fi mayar da hankali kan ƙarfafa da faɗaɗa manyan ayyukan ci gaba da gwamnatin Bala Mohammed ta bari, maimakon ɓata lokaci kan bincike.

Source: Twitter
Tsohon gwamnan ya ce:
“Na yi imani da ci gaba da ayyuka masu amfani ga al’ummar jihar; don haka babu buƙatar ɓata lokaci wajen bincike. Gwamnatin Sanata Bala Mohammed ta yi abin a yaba matuƙa, idan aka duba yawan ayyukan more rayuwa da aka shimfiɗa a faɗin jihar.”
Shawarar tsohon gwamnan Bauchi ga masu takara
Tsohon gwamnan ya kuma yi kira ga duk masu burin tsayawa takarar gwamnan Bauchi a 2027 da su fito da tsayayyen shirin mulki da zai bayyana a sarari irin cigaban da suke son kawowa jihar.
Ya ce:
“Ina kira ga duk masu neman kujerar gwamna su samar da shiri mai jan hankali wanda zai nuna shirye-shiryen ci gaba da suke da su.”
Ahmed Adamu Mu’azu ya ƙara da cewa zai mara wa duk wanda ke da nagartaccen tsari da fahimtar shugabanci baya, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa ba.
A cewarsa:
“Idan kana da kyakkyawan tsari kuma kana son goyon bayana, ka zo mu tattauna. Idan na gamsu, zan goyi bayanka.”
An ware wa limamai, fastoci alawus a Bauchi
A baya, kun ji cewa Gwamnatin Bauchi ta amince da biyan alawus na wata-wata ga limamai da fastoci a faɗin jihar, a wani mataki da gwamnati ta ce zai ƙarfafa haɗin kai a jihar.
Gwamnan jihar, Bala Mohammed, ne ya jagoranci taron majalisar tattalin arzikin jihar, wanda ya gudana a ranar Juma’a, 30 ga watan Janairu, 2026 inda aka cimma matsayar.
Shugaban Ma’aikatan Jihar Bauchi, Barrista Mohammed Sani Umar, ya bayyana cewa majalisar ta tattauna muhimman batutuwa da suka shafi walwalar jama’a da bunƙasar tattalin arziki.
Asali: Legit.ng


