Alkawarin da Abba Kabir Ya Yi ga Wadanda Suka Yi Hatsari a Kano bayan Jajanta Musu

Alkawarin da Abba Kabir Ya Yi ga Wadanda Suka Yi Hatsari a Kano bayan Jajanta Musu

  • Gwamnan Kano, Abba Yusuf, ya nuna alhini bayan rasuwar mutane sama da 30 a mummunan hatsarin mota a Gezawa
  • Hadarin ya faru ne a Kwanar Barde bayan tirela ta yi hatsari sakamakon tukin ganganci, inda mutane da dama suka jikkata
  • Gwamnan ya bayar da umarnin a bai wa wadanda suka jikkata kulawar lafiya kyauta tare da tallafa wa iyalan mamatan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Akalla mutane 30 ne suka rasu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Gezawa.

Hadarin ya auku ne da safiyar Lahadi a yankin Kwanar Barde, cikin karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano.

Kara karanta wannan

'Ba ruwan gwamna': Gwamnatin Sokoto ta magantu kan ba ƴar TikTok gida da mota

Abba ya jajanta wa wadanda suka yi hatsari a Kano
Gwamna Abb Kabir na jihar Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Abba ya yi alhini kan hatsarin mota

Gwamnan ya yi alhini kan lamarin cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Sunusi Bature, ya wallafa a Facebook a yau Lahadi 8 ga watan Fabrairun 2026.

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Yusuf, ya bayyana alhininsa tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu.

Gwamnan ya bayyana cewa lamarin abin tausayi ne sosai, yana mai cewa asarar rayukan babbar rashi ce ga jihar Kano baki daya.

Sanarwar ta ce tirelar na kan hanyarta ne zuwa Gujungu lokacin da ta yi hatsari sakamakon tukin ganganci da direban ya yi.

Gwamnan ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta wa mamatan, ya kuma bai wa iyalansu juriyar jure wannan babban rashi.

Haka kuma ya yi addu’ar samun sauki cikin gaggawa ga duk wadanda ke karbar magani a asibitocin jihar Kano.

Gwamna Abba Kabir ya ɗauki nauyin jinyar wadanda suka yi hatsari
Gwamna Abba Kabir yayin jawabi ga al'ummar Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Umarnin da Abba ya ba ma'aikatan lafiya

Gwamnan ya umarci ma’aikatar lafiya ta jihar Kano da ta tabbatar an bai wa wadanda suka jikkata kulawar lafiya kyauta ba tare da bata lokaci ba.

Kara karanta wannan

Harin Kwara: Kungiyar CAN ta tura muhimmin sako ga Musulmi da aka hallaka

Ya kuma bukaci ofishin mai bai wa gwamna shawara kan harkokin jin kai da ya tantance halin da ake ciki domin tallafa wa iyalan da abin ya shafa.

Sanarwar ta ce:

"Gwamna Yusuf ya yi addu’ar neman Allah ya jiƙan rayukan waɗanda suka rasu, tare da roƙon Allah Ya ba iyalansu ƙarfin guiwar jure wannan raɗaɗin rashin.
" Haka kuma, ya yi addu’ar Allah ya ba da saurin warkewa ga waɗanda ke karɓar magani a asibitoci daban-daban a faɗin jihar.
" Gwamnan ya umarci Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano da ta tabbatar an bai wa dukkan waɗanda hatsarin ya shafa da ke kwance a asibitoci kulawar lafiya kyauta kuma ingantacciya, ba tare da jinkiri ba."

A karshe, gwamnan ya gargadi direbobi, musamman masu manyan motoci, da su guji tukin ganganci tare da bin dokokin hanya.

Abba ya ba yan kasuwar Singer N100m

A baya, mun ba ku labarin cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyara kasuwar Singer domin jajanta wa ‘yan kasuwar da gobara ta shafa da ta jawo masu asarar miliyoyi.

Kara karanta wannan

Bayan kyautar N100m, gwamna Abba ya dauki matakai a kan gobara a kasuwar Kano

Bayan ziyarar da ya kai, Gwamna Abba ya bayyana cewa za a tallafa wa yan kasuwar tare dad daukan matakai don kare afkuwar haka a gaba.

Gwamnati ta bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga waɗanda suka yi asara, sannan an sanar da aikin faɗaɗa da gyaran tituna a kasuwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com