Kanin Ado Aliero Ya Kai Hari Katsina, Sojoji Sun Gwabza Fada da ’Yan Bindiga
- Sojojin Najeriya sun dakile wani yunkurin harin ‘yan ta’adda a Kafur, Jihar Katsina, tare da kwato dabbobi 529 da aka sace
- Rundunar ta yi artabu da ‘yan bindigar da ake zargin sun shigo daga Zamfara, inda aka tilasta musu tserewa da barin dabbobin
- Shugabannin soji sun yaba da jarumta da kwarewar dakarun, suna tabbatar wa jama’a ci gaba da kai farmaki kan masu aikata laifi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Rundunar Sojin Najeriya daga Birged ta 17 da ke Jihar Katsina ta samu nasarar kwato dabbobi 529 da ‘yan ta’adda suka sace.
An kaddamar da wannan aiki ne ta hannun dakarun Forward Operating Base (FOB) Malumfashi, bayan samun sahihan bayanan sirri kan wasu ‘yan bindiga a yankin Kasuwan Sabo da ke Kafur.

Source: Twitter
Sojoji sun samu nasara kan yan ta'adda

Kara karanta wannan
Yadda ƴan ta'adda suka rubuta wa Sarki wasiƙu kan shirin hari kafin hallaka Musulmai a Kwara
A wata sanarwa da mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojin Birged, Kyaftin Abayomi Adisa, wanda aka wallafa a X.
Adisa ya bayyana cewa aikin ya gudana ne ranar Asabar, 7 ga Fabrairu, karkashin jagorancin Kwamandan FOB Malumfashi, Laftanar Kanal M.M. Isa.
Sanarwar ta ce, binciken farko ya nuna cewa ‘yan ta’addan sun shigo yankin ne daga Jihar Zamfara, kuma ana zargin wani mai suna Idi Abasu Aiki, kanin shahararren jagoran ‘yan bindiga Ado Aliero, ne ya jagorance su.
Da zarar sojojin sun isa yankin, ‘yan ta’addan suka bude musu wuta, sai dai dakarun suka mayar da martani da karfin wuta, lamarin da ya tilasta wa ‘yan bindigar tserewa zuwa cikin dazuka.
Sojojin sun bi su har tsakanin kauyukan Burdugau da Unguwan Matau a Karamar Hukumar Malumfashi, inda suka tilasta musu barin dabbobin da suka sace yayin tserewa.
Bayan kammala bincike a yankin, sojojin sun kwato shanu 290, tumaki 238, jaki guda daya da babur guda daya. Rahotanni sun nuna cewa shanu 14 sun mutu yayin artabun, bayan ‘yan bindigar sun yi amfani da su a matsayin garkuwa.

Source: Original
Ba a samu asarar rai daga sojojin ba
Dabbobin da aka kwato an mika su ne ga hukumomin da suka dace domin tantancewa da kuma mayar da su hannun masu su na gaskiya.
Shugaban Karamar Hukumar Kafur, Hon. Suraju Nature, tare da DPO na yankin Kafur, SP Aminu Salihu, ne suka sa ido kan tantancewa da mika dabbobin.
Kwamandan Rundunar Soji ta 8 Division kuma Kwamandan Sector 2 na Joint Task Force, Operation FANSAN YAMMA, Manjo Janar Paul Koughna, ya yaba da jarumtaka da kwarewar dakarun, yana mai jaddada kudirin rundunar sojin na ci gaba da kai farmaki kan masu aikata laifi a yankin Arewa maso Yamma.
Ya kuma tabbatar wa mazauna yankin cewa sojoji za su ci gaba da sintiri domin hana ‘yan ta’adda samun damar motsi a yankunan da suke fakewa.
Yan bindiga sun kashe mutane 20 a Katsina
Kun ji cewa 'yan bindiga sun kai hari garin Doma da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina, sun kashe mutane kuma sun gona gidaje.
Shugaban karamar hukumar Faskari, Sirajo Daudawa ya ce akalla mutane 20 aka kashe a harin duk da sun yi sulhu da 'yan bindiga.
Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa ta tura jami'an tsaro zuwa yankin kuma komai ya daidaita zuwa yanzu.
Asali: Legit.ng

