Yadda Gwamna Ya ‘Hana’ Kashim Shettima Ziyartar Kauyen da Aka Hallaka Musulmi 170
- Gwamnatin Jihar Kwara na fuskantar zargin hana Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ziyartar Woro, inda aka kashe sama da mutum 170
- Rahotanni sun nuna cewa an yaudari Shettima da cewa tafiyar hanyar da nisa, alhali mummunan yanayin hanya ce aka ɓoye masa
- Mazauna yankin sun zargi gwamnati da siyasantar da lamarin, suna cewa an ƙi bai wa iyalan waɗanda aka kashe damar ganawa da Kashim Shettima
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin Kwara - Gwamnatin Jihar Kwara ta sha suka bayan da ake zargin ta da hana Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ziyartar al’ummar Woro.
Woro nan ne garin da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama, inda aka kashe sama da mutum 170 a wani mummunan harin Boko Haram.

Source: Facebook
Gwamnatin jihar Kwara ta tabbatar a shafin Facebook cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya isa Ilorin domin ta'aziyya kan harin 'yan ta'adda.
Zargin da ake yi wa gwamna kan ziyarar Shettima
Majiyoyi daga Fadar Gwamnatin Jihar Kwara sun shaida wa cewa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya yaudari Shettima ta hanyar bayyana masa cewa tafiyar zuwa Woro ta yi tsawo sosai, kuma ba zai iya dawowa Ilorin a rana guda ba.
Sai dai majiyoyin sun ce wannan bayani ba gaskiya ba ne, illa kawai an yi amfani da shi ne don ɓoye mummunan yanayin hanyoyin da ke kaiwa yankin, wanda ke cikin wani hali na lalacewa.
Rahotanni sun nuna cewa domin isa Kaiama daga Ilorin, dole ne matafiya su bi ta Igbeti da Kishi a Jihar Oyo, su shiga Baruten kafin su isa Kaiama, inda kusan dukkan hanyoyin ke cikin lalacewa.
Majiya ta gwamnati ta bayyana Sahara Reporters takaicinta, tana mai cewa wannan mataki ya hana iyalan da ke jimami damar ganin Mataimakin Shugaban Ƙasa a yankinsu da bala’i ya rutsa da su.

Source: Original
Sarki, ciyaman sun shafe kwanaki suna jiran Shettima
Majiyar ta ce maimakon a bar Kashim Shettima ya ziyarci Woro inda aka kashe jama’a, sai aka tara wasu wakilan al’umma aka ce su zo Ilorin su gan shi a can.
Ta kara da cewa:
“Me amfanin ziyarar jaje idan ba a je wurin da abin ya faru ba? Idan da gaske gwamnati na damuwa, me ya hana a samar da jirgin sama mai saukar ungulu ya kai shi kai tsaye?”
Wata majiya ta ce Sarkin Kaiama, Alhaji Mu’azu Shehu Omar, da Shugaban Karamar Hukumar Kaiama sun shafe kwanaki a Ilorin suna jiran zuwan Shettima, cewar Peoples Gazette.
An kuma bayyana cewa Mataimakin Shugaban Ƙasar bai kwashe fiye da mintuna 30 a Ilorin ba kafin ya tafi Owerri domin halartar bikin cika shekaru 50 na Jihar Imo.
Majiyoyin sun ce Shettima ya rasa damar ganawa kai tsaye da waɗanda harin ya shafa, yana mai cewa an siyasantar da bala’in da ya kashe fararen hula marasa laifi.
CAN ta yi jimami harin yan bindiga a Kwara
Mun ba ku labarin cewa kungiyar CAN ta Arewa ta yi kakkausar suka kan kisan gillar da aka yi a Kwara, tana bayyana harin a matsayin rashin tausayi.

Kara karanta wannan
Yadda ƴan ta'adda suka rubuta wa Sarki wasiƙu kan shirin hari kafin hallaka Musulmai a Kwara
Kiristocin sun jaddada cewa lamarin bala’i ne na kasa baki ɗaya, ba na addini ko kabila ba, CAN tana kira da a guji nuna bambanci.
CAN ta yabawa Shugaba Bola Tinubu da jami’an tsaro kan daukar matakin gaggawa, amma ta bukaci gwamnati ta kara tsaurara matakai.
Asali: Legit.ng

