Jakadu da Tinubu Ya Naɗa Sun Shiga Matsala, Ana Iya Kin Karbar Wasu a Ƙasashe
- Wasu ƙasashe na iya ƙin karɓar jakadun Shugaban Najeriya, Bola Tinubu saboda ƙarancin lokacin wa’adin mulkinsa
- Ma’aikatar Harkokin Waje na fama da samun yarjejeniya, yayin da zaɓen 2027 ke gabatowa, abin da ke sa ƙasashen waje nuna jinkiri
- Masana diflomasiyya sun ce jinkirin nadin jakadu kuskure ne, kuma hakan na iya rage tasirin Najeriya a hulɗar ƙasa da ƙasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Babbar matsala na iya tasowa ga wasu daga cikin sababbin jakadun da Shugaba Bola Tinubu ya naɗa.
Ana tunanin za a samu matsalar ce sakamakon yiwuwar ƙasashen su ƙi karɓarsu saboda wa'adin mulkin Bola Tinubu da ya rage.

Source: Twitter
Matsalar da sababbin jakadun Tinubu za su fuskanta
Manyan jami’ai a Fadar Shugaban Ƙasa da ma’aikatan harkokin waje sun bayyana cewa Ma’aikatar Harkokin Waje na fuskantar ƙalubale wajen samun yarjejeniya, cewar Punch.
Sun ce wasu ƙasashe na buƙatar jakada ya samu aƙalla shekara ɗaya ko biyu kafin ƙarshen wa’adin gwamnatin da ta tura shi.
Yayin da zaɓen shugaban ƙasa ke dab da gudana a Fabrairun 2027, wa’adin farko na Tinubu zai ƙare a Mayun shekarar.
Wannan na sa wasu ƙasashe nuna shakku wajen karɓar jakadu da za su yi aiki na ɗan gajeren lokaci.

Source: Facebook
Jami'in diflomasiyya ya magantu
Wani babban jami’in diflomasiyya ya ce wasu ƙasashe kamar Indiya na ganin jakada mai ƙasa da shekara ɗaya na iya haifar da matsala.
Ya ce kafin a samu yarjejeniya, wasu jakadu za su rage da watanni kaɗan kafin ƙarshen wa’adin mulki.
A cewarsa, aikin jakada ƙwararre yawanci na ɗaukar kusan shekaru uku a ƙasa guda, dokar Vienna ta 1961 ta tanadi cewa dole ƙasar da za a tura jakada ta amince kafin a fara aiki, sai dai ƙasar ba lallai ba ne ta bayyana dalilin ƙin amincewa da jakada.
Dalilin Tinubu na janye dukan jakadu a ƙasashe
A Satumbar 2023, Tinubu ya janye dukkan jakadu daga ofisoshin diflomasiyya 109 domin sake fasalin manufofin ƙetare.
Gwamnati ta ce matakin na da nufin inganta inganci da ƙwarewa a harkokin diflomasiyya.
Sai dai wakilan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya da Geneva kaɗai aka bar su saboda taron UN.
Bayan watanni 26, a Nuwambar 2025 ne Tinubu ya tura sunayen jakadu zuwa Majalisar Dattawa domin tantancewa.
Daga baya, shugaban ya ƙara tura wasu sunaye 32, ciki har da jakadun siyasa da na ƙwararru, kamar yadda TheCable ta ce.
A Janairu 2026, an tabbatar da Oke zuwa Faransa, Are zuwa Amurka, Dalhatu kuma zuwa Birtaniya, sauran za su wakilci Najeriya a ƙasashe kamar China, Indiya, UAE, Qatar da Afirka ta Kudu.
Tinubu ya fara tura jakadu zuwa kasashe
A baya, an ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fara tura jakadu zuwa kasashen waje domin wakiltar Najeriya ta fuskar diflomasiyya.
Tinubu ya tura hudu daga cikin jakadu 68 da majalisar dattawan Najeriya ta amince da su a watan Disamban 2025.
Daga cikin jakadun da Shugaba Tinubu ya tura akwai, Ambassada Ayodele Oke, wanda zai wakilci Najeriya a kasar Faransa.
Asali: Legit.ng

