Gwamna Ya Hango Hadari, Ya Rufe Kasuwanni da Tashoshin Mota a Jiharsa
- Gwamnatin Kogi ta rufe kasuwanni da tashoshin mota a kananan hukumomi bakwai domin fatattakar yan bindiga da yan ta'adda
- Matakin yana da nufin katse hanyoyin samun abinci da kayan tallafi ga yan bindiga yayin da jami'an tsaro ke gudanar da samame
- Kwamishinan yada labarai Kingsley Fanwo ya bayyana lokacin da za a bude kasuwannin yayin da gwamnati ta nemi hadin kan jama'a
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kogi - Gwamnatin Jihar Kogi ta sanar da rufe wasu zaɓaɓɓun kasuwanni da tashoshin mota a sassan Kogi ta Yamma.
Wannan mataki wanda na ɗan lokaci ne, an ɗauke shi ne domin gudanar da gagarumin aikin tsaro na fatattakar ƴan ta'adda.

Source: Facebook
An rufe kasuwanni da tasoshin mota
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Kingsley Fanwo, ne ya fitar da sanarwar a yau Lahadi, 8 ga Fabrairu, 2026, in ji rahoton Punch.
Ya bayyana cewa aikin yana gudana ne tare da haɗin gwiwar Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA), Nuhu Ribadu.
Matakin rufewar yana da nufin yanke hanyoyin samun abinci da sauran kayan buƙata ga ƴan bindiga da masu aikata laifuffuka.
Hakan zai hana masu ba da bayanan sirri (infoma) damar tura wa ɓata-garin tallafi yayin da jami'an tsaro ke gudanar da aiki.
Ƙananan hukumomin da abin ya shafa
Wannan umarni ya shafi yankuna daban-daban a cikin ƙananan hukumomi bakwai na gundumar Kogi ta Yamma kamar haka:
A Lokoja, an rufe Oshokoshoko, Jakura, Ogbagbon, Agbaja, Atsawa, Obajana, Apata, Abugi, Amomi, Ebee, da kuma Budon.
A Kabba-Bunu, an rufe Ike Bunu, Ofere, Aiyede, Oke Offin, Agbadu Bunu, Okebukun, da sauran yankunan Bunu baki ɗaya.
Yagba West ta shafi Okoloke, Isanlu Esa, Okunran, Ogbe, Ejiba, Odo Eri, Igbaruku, Ogga, Omi, da kuma Oke Ere.
Yagba East ta haɗa da Irunda Ile, Iyeh Ilotin, Gada, Odogbe, da kuma Ilafin inda aka dakatar da dukkan kasuwanni.
A Kogi (Koton Karfe), an rufe kasuwar shinkafa ta Adingere, Okpareke, Girinya, kasuwar kuɓewa ta Opanda, da kasuwar Edeha.
Mopamuro ta shafi Otafun Amuro, Oroke Amuro, Takete Ide Amuro, Okeagi, Illai, Ilemo, da kuma Ijagbe a wannan karon.
A Ijumu, kasuwannin Ayegunle Gbedde, Iyah Gbedde, Ayetoro Gbedde, Ayeh Gbedde, Iluhagba, Odokoro, da kuma Okoro duk a rufe suke.

Source: Original
Tabbatar da tsaro da buɗe kasuwanni
Gwamnatin ta jaddada cewa an rufe kasuwanni da tasoshin motar ne na ɗan gajeren lokaci domin cin nasarar wannan aiki, cewar sanarwar da aka wallafa a shafin gwamnatin na yanar gizo.
Kwamishinan ya ba da tabbacin cewa za a sake buɗe dukkan kasuwannin da zaran jami'an tsaro sun kammala kakkabe ɓata-garin.
An ɗauki wannan matakin ne sakamakon fargabar tsaro dake ƙaruwa a sassan jihar Kogi da sauran jihohin tsakiyar Najeriya.
Gwamnati ta nemi mazauna yankunan da abin ya shafa da su kwantar da hankalinsu tare da ba wa jami'an tsaro haɗin kai.
Kogi: Gwamna ya rufe makarantu
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Jihar Kogi ta sanar da rufe dukkan makarantu na firamare da sakandare na jihar nan take.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin rigakafin matsalolin tsaro da aka ga suna faruwa.
Fanwo ya bayyana cewa gwamnati ta samu sahihan rahotannin sirri dake nuna bukatar ƙarfafa tsaro a makarantun jihar baki ɗaya.
Asali: Legit.ng


