Shugaba Tinubu Ya Amsa Gayyata zuwa Kasar Birtaniya, Zai Kafa Sabon Tarihi a cikin Shekara 37
- Jirgin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai shilla zuwa Birtaniya domin kai ziyarar aiki a kasar wadda ta yi wa Najeriya mulkin mallaka
- Shugaba Tinubu zai ziyarci Birtaniya ne tare da uwargidansa, Remi Tinubu bayan amsa gayyatar da Sarki Charles ya yi masa
- An bayyana cewa ziyarar da shugaban kasar zai kai zuwa Birtaniya, za ta.gudana ne a cikin watan Maris na shekarar 2026
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyarar aiki zuwa kasar Birtaniya a cikin watan Maris na shekarar 2026.
Shugaba Tinubu ya amince da gayyatar da Sarki Charles ya yi masa domin kai ziyarar aiki zuwa kasar Birtaniya, daga Laraba ranar 18 ga Maris zuwa Alhamis 19 ga Maris, 2026.

Source: Twitter
An sanar da hakan ne ranar Lahadi, 8 ga watan Fabrairun 2026 ta hanyar sakonnin da aka sanya a shafukan UK In Nigeria da Royal Family suka wallafa a manhajar X.

Kara karanta wannan
Atiku Abubakar ya fito ya yi magana bayan Aisha Buhari ta kai masa ziyara a Saudiyya
Tinubu zai kai ziyara zuwa Birtaniya
Shugaba Tinubu zai tafi tare da uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, yayin da Sarki da Sarauniya za su karɓi bakuncin ziyarar a fadar Windsor Castle.
A sakonta, UK in Nigeria ta ce:
“Shugaba @officialABAT ya amince da gayyatar Mai Martaba Sarki domin kai ziyarar aiki zuwa Birtaniya a watan Maris, wacce ita ce ta farko daga wani shugaban Najeriya tun 1989.”
Ofishin ya kara da cewa ziyarar za ta kara karfafa dangantakar haɗin gwiwa mai ɗorewa tsakanin ƙasashen biyu.
Sarki Charles zai karbi bakuncin Tinubu
Haka kuma, shafin Royal Family ya tabbatar da ziyarar inda ya bayyana cewa:
“Shugaban tarayyar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, tare da uwargidansa, Oluremi Tinubu, sun amince da gayyatar Mai Martaba Sarki domin kai ziyarar aiki zuwa kasar Birtaniya daga ranar Laraba 18 ga Maris zuwa Alhamis 19 ga Maris, 2026.”
"Sarki da Sarauniya za su karɓi bakuncin ziyarar a Windsor Castle.”
Ba a bayyana ajandar ziyarar ta ranar 18 ga Maris ba, haka kuma ba a fayyace shirye-shiryen da za a yi ba, sai dai fadar Buckingham ta ce za a sanar da karin bayani a nan gaba.
Fadar shugaban kasa ta tabbatar da ziyarar
Bayo Onanuga ya kuma tabbatar da cewa wannan ita ce ziyarar aiki ta farko da wani shugaban Najeriya zai kai Birtaniya cikin shekaru 37.
"Shugaba Tinubu da uwargidansa za su kasance baƙin Sarki Charles da Sarauniya Camilla daga 18 zuwa 19 ga Maris, 2026."
- Bayo Onanuga

Source: Twitter
Ziyarar aiki uku na karshe da shugabannin Najeriya suka kai Birtaniya sun haɗa da: Yakubu Gowon a 1973, Shehu Shagari a 1981, da Ibrahim Babangida a 1989.
Sarki Charles, a lokacin yana Yariman Wales, ya ziyarci Najeriya a shekarun 1990, 1999, 2006 da 2018.
An bukaci Tinubu ya kori Minista
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu kungiyoyin fararen hula sun mika korafinsu ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Kungiyoyin fararen hular sun bukaci Mai girma Bola Tinubu ya kori Olubunmi Tunji-Ojo daga mukamin Ministan harkokin cikin gida.
Sun bayyana cewa takardun shaidar karatun Tunji-Ojo ba su inganta ba, kuma a cewarsu bai cancanci ya rike mukamin gwamnati ba.
Asali: Legit.ng
