Ana Batun Dokar Zabe, Ribadu Ya Aika da Sakon Gargadi ga 'Yan Siyasa
- Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya yi magana kan zabubbukan da ake tunkara a nan gaba
- Nuhu Ribadu ya aika da sakon gargadi ga 'yan siyasa kan su guji tayar da hankula a lokacin gudanar da zabe
- Mai ba shugaban kasar shawara ya bayyana cewa duk wadanda aka samu da laifi, za su fuskanci fushin hukuma kamar yadda doka ta tanada
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya aika da sakon gargaɗi ‘yan siyasa.
Nuhu Ribadu ya ce duk wanda ke da niyyar tayar da hankali, da kuma masu sayen ƙuri’a, da su guji irin waɗannan ayyuka a zaɓen ƙananan hukumomin Abuja da kuma zaɓubbukan cike gurbi da za a yi a jihohin Rivers da Kano.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Ribadu ya yi wannan gargaɗi ne a yayin taron da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta shirya a Abuja ranar Juma’a, 6 ga watan Fabrairun 2026.
An shirya taron gabanin zaɓen kananan hukumomin Abuja da aka shirya yi a ranar 21 ga Fabrairu, jaridar Vanguard ta dauko labarin.
Wane gargadi Ribadu ya yi wa 'yan siyasa?
Ya yi gargaɗin cewa za a gano duk wani mutum ko ƙungiya da ke da irin wannan shiri, sannan a hukunta su ko a dakile su kafin zaɓe, yayin zaɓe da kuma bayan zaɓe.
Ribadu, wanda daraktan tsaron cikin gida a ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Hassan Abdullahi, ya wakilta, ya yi kira ga jam’iyyun siyasa, ‘yan takara da magoya bayansu da su nuna ladabi da da’a, tare da kiyaye mutuncin tsarin dimokiraɗiyya.
Malam Ribadu ya yi maganganu kan zabe
"Yayin da muke shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin Abuja da kuma zaɓubbukan cike gurbi a jihohin Kano da Rivers, rundunar ‘yan sandan Najeriya, wadda aka ɗora wa alhakin jagorancin tsaron zaɓe, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, na tattara kayan aiki tare da ɗaukar matakai domin hana duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaɓen."

Kara karanta wannan
INEC ta dauki bangare 1 a rikicin PDP, ta yi zama da shugabannin jam'iyyu a Abuja
“Saboda haka, za a tura isassun jami’an tsaro zuwa rumfunan zaɓe da kuma mazabu masu haɗari."
“Haka kuma, za a gano ‘yan daba na siyasa da ‘yan siyasar da ke da halin tashin hankali, a hukunta su ko a dakile su kafin zaɓe, yayin zaɓe da bayan zaɓe, yayin da za a bi diddigin masu sayen ƙuri’a tare da cafke su."
“Saboda haka, ana kira ga jam’iyyun siyasa, ‘yan takara da magoya bayansu da su yi siyasa cikin ladabi tare da kare mutuncin tsarin dimokiraɗiyya. Duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci mai tsanani bisa tanadin doka."
- Nuhu Ribadu

Source: Twitter
Ya kuma yi kira ga kafofin watsa labarai, kungiyoyin farar hula, shugabannin al’umma da kuma ‘yan kasa da su ba da gudunmawa wajen kare dimokuraɗiyyar Najeriya.
Ribadu ya fadi kasashen da ke taimakon Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa Najeriya na samun taimako daga wajen kasashen Turai.
Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewa Najeriya tana samun goyon baya daga kasashen Amurka da wasu ƙasashen Turai wajen yaki da 'yan ta’adda.
Mai ba shugaban kasar shawara kan harkokin tsaron ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu Ribadu ta jajirce wajen kare rayuka da dukiyoyi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

