Sabon Tsarin Albashin Masu Rike da Mukaman Siyasa Ya Je Gaban Tinubu, an Ji Masu Amfana
- Masu rike da mukaman siyasa za su samu karin albashi da alawus bayan kammala sabon tsarin da zai tabbatar da hakan
- Hukumar tattara kudaden shiga da lura da kasafin kudi (RMAFC), ta bayyana cewa an mika sabon tsarin albashin ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
- Shugaban hukumar RMAFC, Mohammed Bello Shehu, ya bayyana wadanda za su ci gajiyar sabon tsarin karin albashin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar tattara kudaden shiga da lura da kasafin kudi (RMAFC) ta yi magana kan karin albashi ga masu rike da mukaman siyasa.
Hukumar RMAFC ta sanar da cewa ta kammala aikin tsara sabon tsarin albashi da alawus-alawus ga masu riƙe da muƙaman siyasa a ƙasar nan.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta ce shugaban RMAFC, Mohammed Bello Shehu, ya bayyana hakan ne yayin kare kasafin kuɗin hukumar a gaban kwamitin kuɗi na majalisar wakilai, a ranar Alhamis, 5 ga watan Fabrairun 2026.
Su wa za a yi wa karin albashi?
Hukumar ta ce ta riga ta miƙa sabon tsarin albashin ga shugaban kasa ta hannun Ofishin sakataren gwamnatin tarayya (OSGF).
Mohammed Bello Shehu ya ce sabon tsarin albashin ya shafi ministoci da sauran masu rike da mukaman siyasa.
Ya ce ana sa ran shugaban kasa zai tura sabon tsarin albashin zuwa majalisar tarayya nan ba da jimawa ba domin dubawa da amincewa da shi, jaridar The Guardian ta dauko labarin.
Ana aiki kan sabon tsarin raba kudaden shiga
Mohammed Bello Shehu ya kara da cewa hukumar na kuma aiki kan sabon tsarin rabon kuɗaɗen shiga, inda ya za a kammala shi cikin wannan shekarar.
Shugaban hukumar, yayin da yake bayar da bayani kan ci gaban da aka samu wajen sake duba tsarin rabon kuɗaɗen shiga tsakanin matakai uku na gwamnati da kuma albashin masu muƙaman siyasa, ya ce:
“Nan ba da jimawa ba za mu kammala. Mun yi duk abin da ya dace. Abin da ya rage kawai shi ne kammala nazarin bayanai sannan mu gabatar da su a gabanku.”
"Muna fatan nan ba da jimawa ba za a tura bukatar hakan zuwa gare ku domin ya zama doka. Amma naku ba sai an yi dokoki ba, wannnan ya shafi ministoci da wasu masu mukamai ne kawai.”
- Mohammed Bello Shehu

Source: Twitter
RMAFC ta koka kan halin gwamnoni
Mohammed Bello Shehu ya kuma nuna damuwa kan tsoma bakin gwamnatocin jihohi a harkokin kuɗi na kananan hukumomi tsawon shekaru.
"Hukumar na son kafa kwamitin kananan hukumomi kamar yadda muke yi a da, kafin Kotun Koli ta ce muna tsoma baki. Yanzu za mu rika sa ido kan kowace karamar hukuma a Najeriya.”
"Ina farin ciki da yadda shugaban kasa ya yi wa gwamnonin jihohi magana, inda ya ce ‘idan ba ku bari ba, zan bayar da umarni'. Saboda haka, hukumar na goyon bayan shugaban kasa gaba ɗaya kan wannan mataki.”
- Mohammed Bello Shehu
Albashin Alkalin Alkalai ya fi na Kashim Shettima
A wani labarin kuma, kun ji cewa Hukumar rarraba kudaden shiga da lura da kasafin kudi (RMAFC), ta yi magana kan albashin Alkalin Alkalan Najeriya.
Hukumar RMAFC ta bayyana cewa Alkalin Alkalan Najeriya (CJN) ya fi mataimakin shugaban kasa samun albashi.
RMAFC ta bayyana cewa alkalai a Kotun Kolin Najeriya sun fi sanatocin da ke wakiltar mazabunsu a majalisar dattawa diban albashi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

