Bayan Shekaru 76, Kotu Ta Yi Hukunci da Gwamnatin Birtaniya Ta Kashe 'Yan Najeriya 21
- Babbar kotun jihar Enugu ta yanke hukunci a kan kisan gilla da Birtaniya ta yi wa wasu ma'aikatan Najeriya a 1949 a bakin aikinsu na hakar ma'adanai
- Kotun ta bayar da umarni ga Birtaniya ta biya diyya fam miliyan 20 ga kowane iyali daga cikin iyalan ma’aikatan kwal 21 da aka kashe
- Kotun ta ce kisan ya saba doka kuma ci mutuncin ran dan adam, tare da umartar Birtaniya ta nemi afuwa, kuma ta buga a jaridu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Enugu – Kotun babbar jihar Enugu ta bayar da umarni ga gwamnatin Birtaniya da ta biya fam miliyan 20 ga kowane iyali daga cikin iyalan wasu ma'aikata da aka kashe.
Rahotanni sun tabbatar da cewa jami'an kasar Birtaniya sun kashe ma’aikatan kwal 21 a ranar 18 ga Nuwamba, 1949 a bakin aiki.

Source: Original
The Cable ta wallafa cewa Mai shari’a Anthony Onovo, wanda ya jagoranci shari’ar a ranar Alhamis, 5 ga watan Fabrairu, 2026 ya ce kisan ya take hakkin dan adam.
Yadda aka fara neman hakkin 'yan Najeriya
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa sun shigar da karar ne ta hannun Greg Onoh, dan gwagwarmayar kare hakkin dan Adam, wanda ya bukaci tabbatar wa Birtaniya laifinta.
Baya ga wannan, ya bukaci a umarci kasar Birtaniya ta nemi gafara tare da biyan diyya mai tsoka ga iyalan wadanda suka mutu.
Wadanda aka shigar da kara sun hada da sakataren harkokin waje na Birtaniya, gwamnatin Birtaniya, gwamnatin tarayya ta Najeriya, babban lauyan kasa, da kuma gwamnatin Birtaniya baki daya.
A hukuncinsa, Mai shari’a Onovo ya ce dole ne a dauki alhakin kisan ma’aikatan kwal tare da biyan diyyakalinta su, domin samar da adalci da gyara ga abin da ya faru.
Umarnin kotu ga Gwamnatin Birtaniya
Kotu ta umarci Birtaniya ta nemi afuwa daga iyalan wadanda abin ya shafa ta hannun lauyoyinsu, tare da wallafa afuwar a jaridun Najeriya da na Birtaniya.
Mai shari’a ya bayyana cewa:
"Wadannan ma’aikatan kwal marasa makami suna neman ingantattun yanayin aiki ne kawai; ba su yi wani yunkuri na tashin hankali ba, amma duk da haka aka harbe su aka kashe su.”
Kotun ta kuma umarci wadanda ake kara na farko, na biyu, na biyar da na shida da su biya fam miliyan 20 ga kowane wanda aka kashe.

Source: Twitter
Jimillar fam miliyan 420 za a biya dukkanin iyalan, kuma an kara kudin ruwa na 10% duk shekara bayan hukunci har sai an biya gaba daya.
Mai shari’a Onovo ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta shiga tattaunawar diflomasiyya da gwamnatin Birtaniya c domin neman adalci da diyya.
Lamarin ya samo asali ne daga yajin aikin da ma’aikatan kwal suka fara a ranar 1 ga Nuwamba, 1949 a Iva Valley, Enugu, saboda bashin albashi da tsauraran yanayin aik.
A lokacin, kwal na daya daga cikin manyan hanyoyin samar da makamashi da kudin shiga ga mulkin mallakar Birtaniya.
Rahotanni sun ce umarnin harbi ya fito ne daga shugaban ‘yan sanda FS Philip, lamarin da ya yi sanadin mutuwar ma’aikata 21 tare da jikkata wasu da dama.
Birtaniya ta magantu kan tsohon sojanta a Najeriya
A baya, mun wallafa cewa gwamnati ta mayar da martani kan bayanin da kasar Birtaniya ta fitar game da rade-radin neman raba Najeriya gida-gida.
Gwamnatin tarayya ta ce Birtaniya ta jaddada cewa ba ta tsoma baki a harkokin cikin gida na wasu ƙasashe, musamman batutuwan da suka shafi ‘yancin kai.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan martani na Birtaniya ya biyo bayan ce-ce-ku-ce da suka taso kan wata wasika da jagoran masu neman ware yankin Yarabawa, Sunday Igboho, ya rubuta wa gwamnatin Birtaniya.
Asali: Legit.ng


