Zance Ya Kare, Hedkwatar Tsaro Ta Yi Magana kan Sojojin Amurka da Aka Turo Najeriya

Zance Ya Kare, Hedkwatar Tsaro Ta Yi Magana kan Sojojin Amurka da Aka Turo Najeriya

  • Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi karin haske kan batun turo sojoji kasar Amurka yi domin taimakawa wajen yaki da ta'addanci
  • Mai magana da yawun hedkwatar tsaro, Manjo Janar Samaila Uba ya ce zuwan sojojin kasar Amurka ba zai taba yancin Najeriya
  • Uba ya jaddada kyakkyawar alakar da ke tsakanin Najeriya da Amurka, inda ya ce kasashen biyu sun dade suna taimaka wa juna a fannoni da dama

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta tabbatar da cewa Amurka ta turo dakarun sojojinta na musamman zuwa kasar nan.

Hedikwatar Tsaron ta bayyana cewa rundunar sojin Amurka mai kula da Afirka (US AFRICOM) ta turo sojoji na musamman cikin Najeriya ne bisa yarjejeniyar da ke tsakanin kasashen biyu.

Babban hafsan tsaro.
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Oluyede Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

Hedkwatar tsaro ta share tantamar 'yan Najeriya

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Bangaren Turaki ya yi bambami bayan INEC ta watsa musu kasa a ido

A rahoton da Vanguard ta tattaro, DHQ ta share tantamar mutane, inda ta ce Amurka ta shigo da sojojin ne bisa tsari da girmama ’yancin Nijeriya.

Daraktan Yada Labarai na DHQ, Manjo Janar Samaila Uba, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai taken, "Karin bayani kan jita-jitar turo dakarun sojojin Amurka zuwa Najeriya".

Sanarwar ta bayyana cewa:

"Hedikwatar Tsaro ta lura da rahotannin kafafen yada labarai da jita-jitar da jama'a ke yadawa game da shigowar dakarun sojojin Amurka cikin Nijeriya.
"Rundunar Tsaron Nijeriya (AFN) tana son bayyana cewa Nijeriya tana da dadadden hadin gwiwar tsaro mai tsari da kasar Amurka."

Hedkwatar ta kara da cewa wannan hadin gwiwa ya ginu ne a kan girmama juna, kuma ya mayar da hankali kan horar da jami'ai, karatun kwarewar sojoji da musayar bayanan sirri da dabarun yaki da ta'addanci.

Alakar Amurka da Najeriya ta kara karfi

A matsayin wani bangare na wannan hadin gwiwa, an gudanar da wani zama na kwanaki biyu tsakanin manyan jami'an gwamnatin Amurka da na Nijeriya a ofishi mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA).

Kara karanta wannan

Da gaske sojojin Amurka sun cafke Sheikh Ahmed Gumi a filin jirgi? Gaskiya ta yi halinta

Wannan taro ya biyo bayan wasu tarurrukan da aka yi a kasar Amurka, wanda ke nuna girman dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu wajen cimma nasara ta zahiri.

Sanarwar ta nuna cewa ana duba wasu shawarwari da nufin karfafa tsaro, kare rayukan fararen hula, da kuma tabbatar da cewa ana yin komai cikin gaskiya da adalci.

Shugaba Tinubu da Donald Trump.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da Shugaba Donald Trump na Amurka Hoto: @aonanuga1956, @DonaldJTrump
Source: Twitter

Hedkwatar Tsaron ta tabbatar wa 'yan kasa cewa duk wata mu'amala da take yi da abokan huldar kasashen waje tana yin ta ne don kare muradin kasa.

Ta kuma kara da cewa hukumomin Najeriya ba za su taba yin wani abu da zai taba ikon Nijeriya na cin gashin kanta ba.

Amurka za ta gina ofishi mai girma a Legas

A wani rahoton, kun ji cewa Amurka za ta kashe kimanin dala miliyan 537 wajen gina ofishin jakadancin da zai zama mafi girma a duniya a birnin Legas, Najeriya.

Wannan babban aiki ba kawai ya shafi gina ofishi ba ne, an ce aikin zai kawo gagarumin ci gaba ga tattalin arziƙin Najeriya ta hanyar zuba jari da samar da ayyukan yi.

Duk da wannan babban jari da Amurka ke zubawa a Najeriya, akwai damuwa a tsakanin ƴan Najeriya dake zaune a Amurka sakamakon tsauraran matakan shige-da-fice na shugaba Donald Trump.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262