An Tafi da Kwankwaso zuwa Kasar Waje Sakamakon Fama da Rashin Lafiya? An Ji Gaskiyar Zance

An Tafi da Kwankwaso zuwa Kasar Waje Sakamakon Fama da Rashin Lafiya? An Ji Gaskiyar Zance

  • Jita-jita ta yadu a kafafen sada zumunta kan batun cewa an tafi da Madugun Kwankwasiyya zuwa kasar waje saboda dalilai na rashin lafiya
  • Mai magana da yawun bakin kungiyar Kwankwasiyya, Mansur Kurugu, ya fito ya yi magana kan jita-jitar wadda aka yada
  • Mansur Kurugu ya ba da tabbacin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bar Najeriya bayan ya halarci wasu tarurruka a ranar Alhamis, 5 ga watan Fabrairun 2026

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Mai magana da yawun ƙungiyar Kwankwasiyya, Kyaftin Mansur Kurugu, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa Rabiu Musa Kwankwaso na fama da rashin lafiya.

Mansur Kurugu ya karyata rahoton da ke cewa an kai jagoran na jam’iyyar NNPP na kasa, zuwa kasar waje domin jinya.

An musanta batun rashin lafiyar Kwankwaso
Jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Mansur Kurugu ya tabbatar da cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya bar Najeriya a ranar Alhamis, 5 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Kano ta kara daukar zafi, an kalubalanci Kwankwaso kan wasu kwangilolin gwamnatin Abba

Tafiyar Kwankwaso ta haifar da jita-jita a kafafen sada zumunta cewa tsohon gwamnan na jihar Kano ya bar kasar ne saboda dalilan rashin lafiya.

Me aka ce kan rashin lafiyar Kwankwaso?

Sai dai da yake mayar da martani kan tambayoyi game da tafiyarsa zuwa kasar waje, Mansur Kurugu ya ce Kwankwaso ya bar Najeriya ne a ranar Alhamis saboda dalilai na kashin kansa.

“Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bar Najeriya ne saboda dalilai na kashin kansa. Ba don yawon neman magani ba ko wata matsalar lafiya.”

- Mansur Kurugu

Wace kasa Kwankwaso ya tafi?

Da aka sake tambayarsa kan inda Kwankwaso ya tafi, Mansur Kurugu ya ce bai san inda ya dosa ba, domin tafiyar ta sirri ce.

Ya danganta jita-jitar da wasu mutane da ke ƙoƙarin karkatar da hankalin jama’a daga gagarumin goyon baya da muhimmancin siyasar Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso a wannan lokaci, jaridar solacebase ta kawo labarin.

“Eh, gaskiya ne Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya fita daga kasar nan, amma tafiyar ta sirri ce, ba ta neman magani ba."

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta yi karin haske a kan zargin Kwankwaso zai koma APC

"Mun kasance tare da shi tsawon jiya da safiyar yau, lokacin da ya karɓi magoya baya daga ƙaramar hukumar Dawakin Kudu da suka kai masa ziyarar goyon baya, daga nan kuma ya wuce Kasuwar Singer.”
"Suna jin haushi ne sakamakon tarin jama’a da Kwankwaso ya ja a manyan tarurruka biyu na ranar, wato ziyarar magoya bayan Dawakin Kudu da kuma yadda aka tarbe shi a Kasuwar Singer."
“Abin mamaki ma, taron jama’ar Dawakin Kudu kaɗai ya fi yawan mutanen da suka tarbi Gwamna Abba Kabir Yusuf lokacin da ya shiga jam’iyyar APC a makon jiya."

- Mansur Kurugu

Kwankwaso ya bar Najeriya bayan kammala tarurruka
Rabiu Musa Kwankwaso na gudanar da jawabi a wajen kaddamar da rundunar tsaron Kano Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Wannan lamari na faruwa ne a daidai lokacin da ake fama da sabani na siyasa tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ubangidansa a siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, biyo bayan sauya shekar gwamnan zuwa jam’iyyar APC.

Kwankwaso ya girgiza kan harin Kwara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi alhinin harin 'yan ta'adda a jihar Kwara.

Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana harin ta'addancin a matsayin dabbanci, inda ya yi Allah wadai kan rasa rayukan mutanen da aka yi.

Madugun na Kwankwasiyya ya ce ya shiga bakin ciki da firgici matuƙa bayan jin labarin yawan mutanen da suka rasa rayukansu a hare-haren.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng