Da Gaske Sojojin Amurka Sun Cafke Sheikh Ahmed Gumi a Filin Jirgi? Gaskiya Ta Yi Halinta
- Ahmed Abubakar Gumi ya musanta rahotannin dake cewa sojojin Amurka sun kama shi a filin jirgin sama yayin da yake kokarin tserewa Turkiyya
- Malamin ya bayyana cewa hoton dake yawo a yanar gizo na bogi ne wanda aka kirkire shi ta hanyar amfani da fasahar zamani ta AI
- Sheikh Gumi ya jaddada cewa yana nan a cikin gida Najeriya kuma zai ci gaba da yada da'awar addini da ta zaman lafiya ba tare da fargaba ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Fitaccen malamin addinin Islama dake Kaduna, Sheikh Ahmed Gumi, ya fito fili ya ƙaryaata rahotannin dake cewa sojojin ƙasar Amurka sun kama shi a wani filin jirgin sama a Najeriya.
Wannan jita-jita ta bazu ne bayan wallafa wani hoto a dandalin sada zumunta wanda ke nuna sojojin Amurka sun iza keyar malamin kamar yana cikin ankwa.

Source: Twitter
Zargin sojoji sun kama Sheikh Ahmad Gumi
Wata ma'abociyar Facebook, Love Haruna ce ta wallafa wannan hoto, inda ta yi ikirarin cewa sojojin Amurka sun cafke Sheikh Ahmed Gumi.
Tare da hoton, Love Haruna ta wallafa cewa:
"Da dumi duminsa.
"Sojojin Amurka da suka shigo Najeriya kwanan nan sun cafke malamin addinin Musulunci, Ahmad Gumi a filin jirgin sama, yayin da ake zargin zai gudu zuwa Turkiya.
"Majiyoyi sun ce an kama Gumi tare da tsari a kokarin da yake yi na gaggauta barin Najeriya biyo bayan zarge-zargen daukar nauyin ta'addanci da aka alakanta shi da su."
Kalli hoton a kasa:
Sheikh Gumi ya karyata batun kama shi
Yayin da yake tattaunawa da jaridar SaharaReporters ta wayar tarho a ranar Alhamis, 5 ga Janairu, 2026, Sheikh Gumi ya bayyana hoton a matsayin "ƙirƙirarren hoto" da aka samar ta hanyar fasahar AI.
Malamin ya nuna mamakinsa kan yadda mutane za su yarda da wannan labari, yana mai cewa sojojin ƙasar waje ba su da ikon kama shi a ƙasarsa ta haihuwa.
Ya bayyana cewa:
“Sojojin Amurka ba za su iya kama ni a Najeriya ba. Me ya sa za su zo su kama ni a Najeriya, kuma a kan wane dalili?”
Sheikh Gumi ya ƙara da cewa:
“Wannan hoton an samar da shi da fasahar AI ne. Ko mutumin da bai sani ba zai gane cewa hoton AI ne.”

Source: Facebook
Halin da Gumi yake ciki yanzu
Sheikh Gumi ya tabbatar wa mabiyansa da sauran ƴan Najeriya cewa yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana nan a kasar ba tare da wani jami'in tsaron Amurka ya kama shi ba.
Malamin ya ce zai ci gaba da gudanar da harkokinsa na addini da na yada da'awar zaman lafiya kamar yadda ya saba ba tare da wata fargaba ba.
Masana fasaha sun gargaɗi ƴan Najeriya da su yi taka tsantsan da hotunan da ake ƙirƙira ta fasahar AI waɗanda aka tsara su don janyo rudani a ƙasa.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun bankawa fadar mai martaba sarki wuta, sun kashe bayin Allah a Kwara
A halin yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga ɓangaren rundunar sojan Amurka ko na Najeriya dake tabbatar da faruwar irin wannan kame.
Gumi ya dage kan tattaunawa da 'yan bindiga
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sheikh Ahmad Gumi ya ce babu wata koyarwar addini ko tsarin tsaro na duniya da ke haramta tattaunawa da ’yan bindiga.
Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa yin sulhu da 'yan bindiga na da fa'ida matuƙar hakan zai hana zubar da jini kuma ya ceci rayukan al’umma.
Malamin ya jaddada cewa Al-Qur'ani ko Injila ba su kawo wani hani na tattaunawa da 'yan bindiga, don haka batun cewa ba a tattaunawa da su ba shi da tushe a addini.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

