Sarki Ya Fasa Ƙwai, Ya Faɗi Kuskuren Sojoji, DSS da Ya Jawo Kisan Mutum 75 a Kwara

Sarki Ya Fasa Ƙwai, Ya Faɗi Kuskuren Sojoji, DSS da Ya Jawo Kisan Mutum 75 a Kwara

  • Sarkin Woro, Umar Bio Salihu ya zargi jami'an sojoji da yin jinkiri na sa’o’i 10 kafin kawo dauki a lokacin da 'yan bindiga suka farmaki al'ummarsa
  • Basaraken ya kuma bayyana cewa ya turawa DSS wata takardar barazana da 'yan bindigar suka aika masa, amma ba a dauki matakin dakile harin ba
  • Basaraken ya yi wadannan 'yan tone tone ne bayan da aka tabbatar da kisan akalla mutum 75 a harin da miyagu suka kai kauyen Wuro da Nuku

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - Sarkin ƙauyen Woro dake jihar Kwara, Umar Bio Salihu, ya fito fili ya soki jami'an tsaro kan jinkirin da suka yi na tsawon sa'o'i 10 kafin su kawo ɗauki yayin da ake kisan kiyashi a garinsa.

Basaraken ya bayyana cewa gazawar jami'an tsaro da kuma matsalar bayanan sirri ne suka ba ƴan ta'adda damar kashe mutanen da suka haura 75 a garin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mutane 10, sun kona gidaje a sabon harin da suka kai Kwara

Sarkin kauyen Woro ya fadi yadda sojoji suka ki kai masu dauki da wuri har aka kashe mutum 75
Wata mata zaune a kusa da kangon gidanta a kauyen Kawuri, jihar Borno bayan harin Boko Haram da ya yi ajalin mutum 70. Hoto: STRINGER / Getty Images
Source: Getty Images

Umar Bio Salihu, ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da gidan talabijin na Arise News a yau, 5 ga Fabrairu, 2026.

Bayanin Sarkin Woro kan jinkirin sojoji

Basaraken ya ce sun fara kiran neman ɗauki tun ƙarfe 5:00 na yamma sa'ilin da 'yan bindigar suka shiga garin, amma sojoji ba su kai daukin ba ba sai ƙarfe 3:00 na dare bayan maharan sun gama komai sun tafiya.

Umar Bio Salihu ya nuna takaicinsa kan yadda rundunar sojoji ta bar garin ba tare da kariya ba bayan an janye dakarun da aka jiye masu watanni biyar da suka gabata.

Sarkin ya bayyana cewa:

“Na kira su tun bayan ƙarfe 5:00 na yamma, amma ba su zo ba sai ƙarfe 3:00 na dare. Wannan jinkiri na sa’o’i 10 ya ba 'yan ta'addar damar cin karensu ba babbaka.”

Basaraken ya ƙara da cewa lokacin da sojojin suka iso, maharan sun riga sun tsere, kuma babu wani jirgin yaƙi da ya kawo ɗauki ko ya harbi ƴan ta'addan duk da kiran da aka yi.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun nuna bajinta, sun hana 'yan bindiga sakewa a Sokoto

"Sojoji ba su fafata da 'yan ta'adda ba' - Sarki

Sarki Umar Bio Salihu ya bayyana cewa:

"Sojoji ba su farmake su ba. 'Yan bindigar sun riga sun kama gabansu lokacin da sojojin suka zo.
"Jirgin yakin sojojin sama ma bai farmake su ba. Babu wata fafatawa da suka yi. Ba su saukar da wani bam ko harba masu bindiga ba.
"Da fari, muna da sansanin sojoji a yankin. Akwai akalla sojoji 15 da aka girke. Amma kimanin watanni biyar baya, 'yan bindiga suka farmaki sojojin. Tun daga lokacin ne aka janye su. Ba mu da wani jami'in tsaro a yankin.
"Wannan ya ba 'yan ta'addar damar kawo mana a duk lokacin da suka ga dama, su zo su ci karensu ba babbaka, babu mai iya yin komai a kai."
Sarkin Woro ya ce sun sanar da DSS kafin a kawo harin amma ba a dauki mataki ba har aka kashe mutum 75
Taswirar Kwara, jihar da 'yan bindiga suka kashe akalla mutum 75 a harin da suka kai Woro da Nuku. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Bankaɗo matsalar bayanan sirri

Babban abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda basaraken ya ce ya tura wa jami'an DSS wasiƙar barazana da ƴan ta'addan suka aiko masa, amma hakan bai hana harin faruwar ba.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun bi sawun dan kasuwar Kano, sun ɗauke shi a jihar Nasarawa

Ya nuna fargabar cewa watakila an samu kuskure wajen sarrafa bayanan sirrin, wanda hakan ya harzuƙa ƴan ta'addan na ƙungiyar Mamuda har suka ƙaddamar da harin, suka kashe mutane.

A cewar sa, ƴan ta'addan sun fusata ne saboda al'ummar garin sun ƙi karɓar akidarsu ta ta'addanci, sannan kuma sun ga babu sojoji a kusa da zasu kare su.

Tinubu ya tura bataliyar sojoji Kwara

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin tura bataliyar sojoji zuwa Woro a karamar hukumar Kaiama, jihar Kwara domin dakile ‘yan bindiga.

Harin da aka kai ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, inda rahotanni suka nuna sabani a alkaluman wadanda suka rasu, abin da ya kara tayar da hankali.

Gwamnatin tarayya ta yi kira ga hadin kai tsakanin hukumomin tsaro da na jihohi domin taimakon al’umma da hukunta masu aikata laifuffuka a fadin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com