Bayan Zuwan Dakarun Amurka, Sojojin Faransa Sun Hadu da na Najeriya a Abuja
- Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ta sake jaddada ƙudirinta na ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da Faransa domin inganta horaswa, musayar bayanan sirri da kuma ƙwarewa
- Laftanar Janar Waidi Shaibu ya bayyana cewa haɗin gwiwa da Faransa zai taimaka wajen gina ƙwarewa da fuskantar sababbin barazanar tsaro na zamani a Najeriya
- Wani jami’in Faransa a Najeriya, Kanal Stéphane Useo, ya yaba da jajircewar sojojin Najeriya tare da tabbatar da aniyar ƙasar sa na ci gaba da tallafa wa ƙoƙarin inganta tsaro
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ta ce tana ƙara faɗaɗa haɗin gwiwar tsaro da ƙasar Faransa a wani yunkuri na ƙarfafa tsaron ƙasa da kuma samar da zaman lafiya mai ɗorewa a Yammacin Afirka.

Kara karanta wannan
Sarki Sanusi II ya fadi dalilan da suka sa ba zai yi shiru a kan harkokin gwamnati ba
Wannan ya fito ne bayan wata ganawa da Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya yi da jami’in tsaron Faransa a Najeriya, Kanal Stéphane Useo, a hedikwatar rundunar soji da ke Abuja.

Source: Facebook
Rundunar Najeriya ta wallafa a X cewa ganawar ta mayar da hankali kan hanyoyin da za a bi wajen inganta horaswa, musayar bayanan sirri da kuma ƙara ƙwarewar aiki.
Bayanin da sojojin Najeriya suka yi
A yayin ganawar, Laftanar Janar Waidi Shaibu ya sake jaddada aniyar rundunar sojin Najeriya na ci gaba da bunƙasa ƙwarewar jami’anta a dukkan sassa na rundunar.
Vanguard ta rahoto ya ce haɗin gwiwar tsaro da Faransa na da matuƙar muhimmanci, musamman wajen samar da horo na zamani da dabarun aiki da suka dace da sabon yanayin barazanar tsaro.
Babban hafsan ya nuna fatan cewa ƙulla haɗin gwiwa da Faransa zai taimaka wajen ƙara ƙarfin rundunar sojin Najeriya, ta fuskar dabarun yaki, ingantaccen tsari da kuma aiwatar da ayyuka cikin kwarewa.
Gudummawar kasar Faransa ga Najeriya
Laftanar Janar Shaibu ya yaba wa Faransa bisa ci gaba da bayar da gudunmawa ga rundunar sojin Najeriya, musamman a bangaren musayar bayanan sirri, horas da sojoji da kuma tallafin ayyukan tsaro.
Ya ce irin wannan haɗin gwiwa na taimaka wa Najeriya wajen tinkarar barazanar tsaro da ke addabar yankin, tare da ƙarfafa ikon rundunar wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Bayanin wani jami’in tsaron Faransa
A nasa jawabin, Kanal Stéphane Useo ya yabawa rundunar sojin Najeriya bisa jajircewa da himma wajen fuskantar sababbin ƙalubalen tsaro.
Ya ambaci nasarorin da sojojin Najeriya suka samu a wasu ayyukan dawo da zaman lafiya a yankuna, ciki har da farmakin da aka kai wajen hana juyin mulki a Benin..

Source: Facebook
Kanal Useo ya buƙaci a faɗaɗa damar horaswa a manyan kwasa-kwasan soja, musamman a fannoni irin su hulɗar jama’a da harkokin jiragen sama,.
Ya yaba da kafa Makarantar Hulɗar Jama’a ta Sojin Ƙasa a matsayin ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin horaswa a Afirka.
Sojojin Amurka sun yaba wa Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Rundunar sojin Amurka da ke lura da Afrika ta yaba wa Najeriya bisa rawar da ta ke takawa wajen yaki da ta'addanci.
Rundunar ta bayyana cewa Najeriya na cikin kasashen da suke taka rawar gani wajen yaki da 'yan ta'addan ISWAP da Al-Qa'ida.
Kwamandan AFRICOM ya yaba wa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kan yadda ya ke bayar da hadin kai wajen yaki da ta'addanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
