Dokar Zabe: Majalisar Dattawa Ta Cimma Matsaya kan Tura Sakamako Ta Yanar Gizo

Dokar Zabe: Majalisar Dattawa Ta Cimma Matsaya kan Tura Sakamako Ta Yanar Gizo

  • A karshe dai Majalisar dattawan Najeriya ta zama domin amincewa da yin gyara a dokar zabe ta Najeriya da ake amfani da ita
  • A yayin zama don duba dokar zaben, 'yan majalisar dattawa sun tattauna kan batun tilasta tura sakamakon zabe ta hanyar yanar gizo
  • Bayan an gama muhawara, sanatocin sun bukaci a ci gaba da amfani da tsarin da ake bi wajen tura sakamakon zaben da aka kada

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta Najeriya ta ƙi amincewa da ƙudirin da ke neman tilasta tura sakamakon zaɓe ta hanyar yanar gizo.

Majalisar dattawan ta yi watsi da gyaran da aka gabatar kan sashe na 60(3) na Kudirin gyaran dokar zaɓe wanda yake bukatar kwaskwarima.

Majalisar dattawa ta ki amincewa da kudirin tura sakamakon zabe
Godswill Akpabio da sauran sanatoci yayin zaman majalisar dattawa Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Rahoton tashar Channels tv ya nuna cewa majalisar dattawan ta cimma matsayar ne a yayin zamanta na ranar Laraba, 4 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta rufe bakin masu surutu, ta yi gyara a dokar zaben Najeriya

An so majalisa ta yi gyara a dokar zabe

Gyaran, wanda aka tattauna a zaman majalisa, ya yi nufin tilasta wa jami’an INEC da ke jagorantar rumfunan zaɓe su tura sakamakon rumfar zaɓe kai tsaye ta yanar gizo zuwa na'uara IREV.

A ƙarƙashin ƙudirin, tura sakamakon zai gudana ne bayan an cika sakamakon a takardar EC8A, jami’in ya sa hannu da hatimi, tare da sa hannun wakilan jam’iyyun siyasa.

'Yan majalisa sun ki amincewa da bukatar

Sai dai ’yan majalisar sun ƙi yin na'am da wannan tanadi, inda suka bar tsohon tsarin dokar zaɓe yadda yake.

A halin yanzu, dokar da ke aiki ta bai wa INEC cikakken iko na tantance yadda ake tura sakamakon zaɓe.

Dokar ta yi tanadin jami’in rumfar zaɓe ne zai tura sakamakon, ciki har da adadin masu kada ƙuri’a da aka tantance da kuma sakamakon kuri’un, ta hanyar da hukumar INEC ta tanada.

Da wannan mataki, majalisar dattawa ta ci gaba da kare ikon INEC na zaɓar hanyar tura sakamakon, maimakon tilasta dora sakamakon ta hanyar yanar gizo zuwa na'uarar IREV a matsayin wajibi na doka, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta samu koma baya, sanatocin jihar Taraba sun sauya sheka zuwa APC

Majalisa ta ki amincewa da karin shekarun dauri

Tun da farko, majalisar dattawa ta kuma ki amincewa da kudirin hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari ga masu saye da sayar da katin zaɓe na dindindin (PVC) a karkashin sashe na 22.

Majalisar dattawa ta ki amincewa da gyara kan tura sakamakon zabe
Sanatoci yayin zaman majalisar dattawa Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Majalisar ta bar hukuncin daurin shekaru biyu, amma ta kara tarar kuɗi daga Naira miliyan 2 zuwa Naira miliyan 5.

Haka kuma, ’yan majalisar sun gyara sashe na 28 da ya shafi sanarwar zaɓe, inda suka rage wa’adin daga kwanaki 360 zuwa kwanaki 180.

A sashe na 29, majalisar ta kuma rage wa’adin mika jerin ’yan takara da takardunsu daga jam’iyyun siyasa daga kwanaki 180 zuwa kwanaki 90.

Atiku ya zargi majalisa da shirya magudi

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya jefa zargi ga majalisar tarayya kan dokar zabe.

Atiku ya ce majalisar dattawa ta shimfida hanya domin magudin babban zaben shekarar 2027 ta hanyar jinkirta gyaran dokar zabe ta 2022.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce gibin da ke cikin dokar zaben da ake amfani da ita yanzu ya taka rawa sosai wajen matsalolin da suka biyo bayan zaben 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng