Harin 'Yan Bindiga a Katsina Ya Girgiza Majalisa, Ta Mika Bukata wajen Tinubu

Harin 'Yan Bindiga a Katsina Ya Girgiza Majalisa, Ta Mika Bukata wajen Tinubu

  • 'Yan bindiga sun ci gaba da kai hare-haren ta'addanci a wasu yankunan jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Majalisar dattawan Najeriya ta nuna damuwarta kan yadda 'yan bindiga ke ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankunan
  • Ta mika bukatarta ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan abin da take son a yi a yankunan domin dakile matsalar rashin tsaro

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a jihar Katsina bayan sababbin hare-haren ’yan bindiga da suka yi sanadin mutuwar akalla mutane 35 cikin awanni 24.

Majalisar dattawan ta yanke shawarar neman gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa na sojoji da kai kayan jin-kai a yankunan da abin ya shafa.

Majalisar dattawa ta koka kan rashin tsaro a Katsina
Sanatoci yayin zaman majalisar dattawa Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta ce majalisar ta cimma wannan matsayar ne yayin zamanta na ranar Laraba, 16 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Ana murna sulhu ya fara aiki, 'yan bindiga sun shiga gari sun kashe akalla mutune 20

Wannan matsayar ta biyo bayan kudirin gaggawa kan harin kwanton ɓauna da aka yi wa jami’an rundunar 'yan sanda a karamar hukumar Bakori, inda ’yan sanda uku suka mutu yayin da biyu suka jikkata.

Sanata ya koka kan rashin tsaro a Katsina

Da yake jagorantar muhawarar, Sanata Mohammed Dandutse, mai gabatar da ƙudirin, ya ce Majalisar ta damu matuƙa da yawaitar hare-haren da ke faruwa a al’ummomi daban-daban na Katsina.

Ya bayyana cewa zuwa ranar Talata, 3 ga Fabrairu, 2026, akalla mutane 35 suka rasa rayukansu a hare-hare da aka kai a kananan hukumomi da dama.

A cewarsa, an kashe mutane 24 a ƙaramar hukumar Faskari, takwas a Dandume, biyu a Funtua, da ɗaya a Kankara, duk cikin awanni 24 kacal, jaridar The Punch ta kawo labarim.

Ya yi gargaɗin cewa ci gaba da hare-haren a yankunan karkara na yin mummunan tasiri ga noman abinci, inda aka ce fiye da gonaki 50,000 aka yi watsi da su saboda rashin tsaro, lamarin da ke barazana ga wadatar abinci da hanyoyin samun abin rayuwa a jihar.

An kai korafi gaban Shugaba Tinubu

Sanatan Kudancin Katsina ya kuma tuna cewa Gwamnan Katsina, Dikko Radda, ya taba jagorantar tawagar dattawan Yankin Funtua zuwa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin yi masa bayani kan halin tsaro.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bankawa fadar mai martaba sarki wuta, sun kashe bayin Allah a Kwara

“A wannan ziyara, shugaban kasa ya yi alƙawarin kafa barikin sojoji a yankin, musamman a kusa da Malumfashi, domin dakile ’yan bindiga."

- Sanata Mukhtar Dandutse

Ya nuna damuwa kan yadda ’yan ta’adda ke cin gajiyar hanyoyin shiga-da-fita marasa tsaro da ke haɗa Katsina da wasu sassan Kaduna da Zamfara, ciki har da Machika, Kankara da sauran hanyoyin dazuzzuka, yana jaddada buƙatar ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin jihohi.

Muntari Dandutse ya koka kan matsalar rashin tsaro
Sanata mai wakiltar Katsina ta Kudu a majalisar dattawa, Muntari Dandutse Hoto: Habib Maigora
Source: Facebook

Wace matsaya majalisa ta cimmawa?

Bayan kammala muhawara, Majalisar Dattawa ta amince baki ɗaya da ƙudirin, tare da:

  • Kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta aiwatar da alƙawarinsa na kafa sabon barikin sojoji a yankin da abin ya shafa na Katsina.
  • Umartar Sufeton-Janar na ’yan sanda da ya tanadarwa rundunar ’yan sanda a yankin motoci masu sulke aƙalla guda uku, domin ƙarfafa ayyukan tsaro bisa bayanan sirri, binciken dazuzzuka.
  • Kira ga hukumomin tsaro da su ci gaba da ayyukan haɗin gwiwa har sai an kakkabe dukkan ’yan ta’adda a Katsina da makwabtan wuraren da ke da matsala.
  • Umarni ga ma’aikatar jin-kai ta tarayya da hukumar NEMA da su kai agajin gaggawa ga iyalai da al’ummomin da abin ya shafa da kuma waɗanda suka shiga firgici.

Kara karanta wannan

Bayan turo sojoji Abuja, Amurka ta yi maganar yakar 'yan ta'adda a Najeriya

Turji ya saki tsohon dan bindiga a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani tsohon fitaccen jagoran 'yan bindiga a Katsina, Audu Lankai, ya shaki iskar 'yanci bayan yaran Bello Turji sun sace shi.

Yaran na Bello Turji sun kama Lankai ne bayan rikici da ya taso sakamakon gazawar wata mu’amalar sayar da makamai.

Mazauna yankin Jibia sun bayyana cewa a baya-bayan nan ya zama jigo wajen sulhunta ƙungiyoyin 'yan bindiga da al’umma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng