Sanusi II Ya Yi Gargadi ga Maza Masu Dukan Mata da Auren Wuri a Najeriya
- Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce babu wata al’ada da ke ba wa namiji damar dukan mace, yana jaddada cewa mata ‘yan ƙasa ne masu cikakken ‘yanci
- Sanusi II ya bayyana cewa wasu maza na amfani da karfin iko da suke da shi wajen cin zarafin matan da suke karkashinsu wanda hakan ya ce bai dace ba
- Mai martaban ya danganta auren wuri da ake yi wa mata da talauci da rashin damar samun ilim, ba wai al’ada da ake cewa mutane na rayuwa a kanta ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas – Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi Allah-wadai da duk wani nau’in cin zarafi da ake yi wa mata a cikin al’umma, yana mai cewa ba za a taba yarda da hakan ba.
A cewarsa, mata na da matsayi mai muhimmanci wajen gina ƙasa, kuma dole ne a buɗe musu ƙofofi domin inganta rayuwarsa a Najeriya.

Source: Facebook
Sarkin ya bayyana haka ne yayin wata hira a shirin Morning Brief na tashar Channels Television, inda ya tattauna kan muhimman batutuwan shafar ƙasa.
Maganar Muhammadu Sanusi II kan mata
Sarkin ya ce ba daidai ba ne namiji ya rika dukan mace ko cin zarafinta da hujjar cewa al’ada ta ba shi dama. Ya jaddada cewa mata ‘yan ƙasa ne na Najeriya, kuma doka ta tanadi kariya gare su kamar kowa.
Sanusi II ya ce a cikin al’umma, masu rauni su ne suka fi fuskantar cin zarafi, ciki har da mata, yara ƙanana, talakawa da masu bukata ta musamman.
Ya kara da cewa dukan mata da duk wani na'u'i na cin zarafi ba al'ada ba ce ta Afrika, ya ce wasu ne suka samu karfin iko suke wuce gona da iri.
Batun ilimin mata da auren wuri
Sanusi II ya kuma tabo batun auren wuri, inda ya ce yawancin ‘yan mata na kammala firamare, amma basu da wata hanya ta ci gaba da karatu ko koyon sana’a.
A cewarsa, wasu yankunan Arewa na da makarantun firamare amma babu sakandare, babu cibiyar koyon sana’a, kuma babu wani tsari da aka tanada don makomar yara masu tsakanin shekaru 11 zuwa 18.
Ya bayyana cewa a irin wannan yanayi, iyaye talakawa kan yanke shawarar aurar da ‘ya’yansu mata ba wai don son rai ba, sai don tsoron abin da zai iya faruwa sakamakon rashin kulawa da talauci.

Source: Facebook
Sanusi II ya ce galibin waɗannan al’adu na auren wuri suna da alaƙa da talauci da rashin tsari daga gwamnati, yana mai kira da a samar da ilimi, sana’o’i ga ‘yan mata domin rage matsalar auren wuri da cin zarafin mata.
Ga bayanin da ya yi a kasa:
Sanusi II ya je taron sarakuna Legas
A wani labarin, mun kawo muku cewa Mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II ya halarci wani taron sarakuna da aka yi a jihar Legas.
Taron ya samu halartar manyan shugabannin kugiyoyin duniya, gwamnatin jihar Legas da manyan sarakuna a ciki da wajen Najeriya.
Legit Hausa ta gano cewa shugabanni sun mayar da hankali kan yadda za su magance matsalar cin zarafin mata da yara kanana a Afrika.
Asali: Legit.ng

