Abin da Ya Hana Epstein Kasuwancin Mai a Najeriya, Ya Shirya Ganawa da Jonathan

Abin da Ya Hana Epstein Kasuwancin Mai a Najeriya, Ya Shirya Ganawa da Jonathan

  • Sababbin takardun hukumar FBI sun nuna Jeffrey Epstein ya taba shirin cinikayyar danyen mai da Najeriya
  • Sakon Imel ya bayyana yadda aka yi masa alkawarin ribar dala miliyan shida daga sayar da man Najeriya zuwa China
  • Takardun sun kuma fallasa hulɗar Epstein da manyan mutane a duniya, ciki har da shugabannin siyasa, da manya a cikin gwamnatin Amurka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wasu sababbin takardu da aka fitar sun bayyana kan Jeffrey Epstein, wanda aka taba samu da laifin cin zarafin yara ta hanyar jima’i.

Takardun sun ce Jeffrey Epstein ya yi yunƙurin shiga harkar cinikayyar danyen man fetur a Najeriya, sai dai yana tsoron a yaudare shi.

An 'gano' Epstein na fasa cinikayyar mai a Najeriya
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da Jeffrey Epstein. Hoto: Goodluck Jonathan, Neil Rasmus/Patrick McMullan.
Source: Getty Images

Ana ci gaba da bankado takardun Epstein

Takardun da jaridar Premium Times ta samu, na daga cikin manyan bayanai da Hukumar FBI ta Amurka ta fitar karkashin dokar 'Epstein Files Transparency Act'.

Kara karanta wannan

Tonon asiri: Yadda ɗan Najeriya ya damfari baturiya $2.5m da sunan yariman Dubai

A cikin wata tattaunawar imel da aka yi a ranar 20 ga Satumba, 2010, wani mutum mai suna David Stern ya sanar da Epstein wata damar kasuwanci da zai iya samun riba mai yawa ta hanyar saye da sake sayar da danyen man Najeriya.

Stern ya ambaci wani mutum da ake kira “PA” wanda ya ba da shawarar a hadu da wasu da ke da damar sayen man Najeriya da kuma sake sayar da shi zuwa China, inda aka kiyasta ribar da za a samu har dala miliyan shida.

A cikin sakon, Stern ya rubuta cewa:

“PA ya nemi na gana da wani mutum da ke da damar samun man Najeriya, idan aka sayar da shi zuwa China ko wani wuri, za a iya samun kusan dala miliyan 6.”

Sai dai duk da wannan alkawari, an nuna shakku kan yarjejeniyar, Stern ya bayyana cewa lamarin akwai alamar damfara, inda ya ce:

“Wannan lamari yana da matukar shakku, kamar yadda shugabana JEE zai fada.”

Wannan tattaunawar ta imel na daya daga cikin daruruwan sakonni da Epstein ya yi da mutane masu karfi da kudi kafin mutuwarsa a shekarar 2019.

Takardun sun nuna cewa ana yawan ambaton Najeriya a cikin hirarrakin da suka shafi kasuwanci, zuba jari da tafiye-tafiye.

Kara karanta wannan

Bayan turo sojoji Abuja, Amurka ta yi maganar yakar 'yan ta'adda a Najeriya

Ana ci gaba da bankado sirruka kan takardun Epstein
Marigayi Jeffrey Epstein da ke da alaka da manyan duniya kafin rasuwarsa. Hoto: @gaming_leaker.
Source: UGC

Shirin ganawar Epstein da Goodluck Jonathan

Haka kuma, a shekarar 2010, Epstein ya samu wani imel daga George Reenstra, wanda ya kafa kamfanin jirage, inda ya sanar da shi cewa zai ziyarci Najeriya domin ganawa da shugaban kasa a wancan lokaci, Goodluck Jonathan.

Reenstra ya bayyana cewa ganawar dole ce, duk da cewa tafiyar ba a tsara ta ba tun farko, sai dai babu tabbacin cewa ganawar ta gudana.

Takardun sun kuma bayyana sunayen manyan mutane da Epstein ya yi mu’amala da su, ciki har da Bill Clinton, Elon Musk, da Yariman Birtaniya, Prince Andrew.

Har ila yau, an gano hulɗarsa da wasu na kusa da shugaban Amurka, Donald Trump, kodayake ya ce ya raba alaka da Epstein tun da dadewa, cewar BBC News.

Bayan mutuwar Epstein a gidan yari a 2019, an ci gaba da ganin matsin lamba daga jama’a domin a fitar da cikakkun bayanan takardunsa, domin a fahimci girman laifuffukan da kuma dangantakarsa da masu iko a duniya.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Atiku ya yi ganawar sirri da babban Sanatan APC Abdulaziz Yari

An fadi dalilin Jonathan na korar ministansa

Kun ji cewa tsohon ministan Matasa da wasanni a mulkin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fadi dalilin rasa kujerarsa bayan kamfe.

Bolaji Abdullahi ya ce Jonathan ya cire shi daga mukamin minista saboda ya ki sukar Bukola Saraki a yakin neman zaben shekarar 2015.

Ya bayyana hakan ne a Abuja yayin kaddamar da littafinsa, inda ya ce an matsa masa lamba ya soki kan Saraki bayan ya koma APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.