Sanusi II Ya Hallara Taron Sarakunan Afrika, ba a Ga Aminu Ado ba
- Khalifa Dr Muhammad Sanusi II ya halarci wani babban taron nahiyar Afirka da aka shirya domin duba rawar sarakuna kan kare hakkin dan Adam
- Taron ya tara manyan sarakuna da shugabannin gargajiya daga ƙasashe daban-daban na Afirka tare da manyan jami’ai da ƙungiyoyin duniya
- An tattauna hanyoyin sauya dabi’u da al’adu da kuma yadda za a haɗa sarakuna cikin tsare-tsaren ƙasa da yankuna wajen hana cin zarafin mutane
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas – Khalifa Dr Muhammad Sanusi II ya halarci wani muhimmin taro na musamman da ya hada sarakunan Afrika a birnin Lagos.
An gudanar da taron ne a ranar Litinin, 3, Fabrairu, 2026, a otal din Radisson Blu da ke Ikeja, inda aka tara manyan sarakuna da shugabannin gargajiya daga sassan Afirka.

Source: Facebook
Shafin Sanusi II Dynasty ya wallafa a Facebook cewa gidauniyar Ford Foundation tare da UN Women da gwamnatin tarayya ne suka shirya taron domin tattauna rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen hana cin zarafin dan Adam.
Matsayar Muhammadu Sanusi II da sarakuna
The Cable ta rahoto cewa a yayin taron, sarakunan Afirka sun jaddada aniyarsu ta ƙara ƙaimi wajen hana cin zarafin dan Adam a cikin al’ummominsu.
Sun bayyana cewa sarakuna na da muhimmiyar rawa wajen sauya tunanin al’umma da gyara dabi’un da ke haddasa tashin hankali.
Sarki Sanusi II ya halarci zaman tattaunawa da sauran manyan sarakuna, inda aka yi nazari kan yadda za a yi amfani da al’adun gargajiya wajen kare mata da yara.
An jaddada cewa al’adu ba su amince da zalunci ba, kuma duk wani tsari da ke cutar da dan Adam ya sabawa ginshikin rayuwar al’umma.
Manyan baki da sarakuna a taron
Taron ya samu halartar Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu, da Ooni na Ife, Adeyeye Ogunwusi, da Sarkin Fika, Sarkin Shonga, da Obi na Onicha, da kuma sarakuna daga Nijar, Ghana, Burkina Faso, da Zimbabwe.
Shugabar gidauniyar Ford Foundation, Heather Gerken, tare da jami’an UN Women, sun yi jawabi kan muhimmancin haɗin kai tsakanin sarakunan gargajiya da hukumomi.
Sarkin Shonga, Haliru Yahaya Ndanusa, ya yi gargadi kan amfani da addini wajen halasta tashin hankali, yana mai cewa duk wani aiki da ke cutar da dan Adam ya saba wa koyarwar addini.

Source: Facebook
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mohamed Fall ya bukaci sarakuna da su yi amfani da tasirinsu wajen kare rayuka da tsayar da adalci da daidaito a cikin al’umma.
Sanusi II ya koma Kano daga Legas
A wani labarin, kun ji cewa Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II ya koma jihar Kano bayan wata tafiya da ya yi zuwa jihar Legas.
Rahotanni sun nuna cewa Sarkin ya ziyarci Legas ne domin yin ta'aziyya ga iyalan Sanata Bukola Saraki bayan rasuwar surikinsa.
Sanusi II ya koma Kano ne jim kadan bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya ayyana shi a matsayin halastaccen Sarki maimakon Aminu Ado Bayero.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

