Maina: Tsohon Shugaban Gyaran Fansho Ya Fadi a Abuja, An Wuce da Shi Asibiti
- Tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho, Dr Abdulrasheed Maina, ya faɗi a Abuja, inda aka garzaya da shi asibiti cikin gaggawa
- Rahoto ya ce Maina ya faɗi ne sakamakon matsalar raunin gwiwa da ba a kula da shi ba, lamarin da ya sa ya fadi kasa
- Likitoci sun ce ana iya shirya jigilar sa idan lafiyarsa ba ta daidaita cikin lokaci kaɗan domin tabbatar da ba shi kulawa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - An garzaya da tsohon shugaban kwamitin gyara fasalin fansho, Dr Abdulrasheed Maina wani asibiti mai zaman kansa a Abuja.
Lamarin ya faru ne a daren Talata 3 ga watan Faburairun 2026 bayan ya faɗi yayin da yake ƙoƙarin shiga harabar ofishinsa a birnin Abuja.

Source: Facebook
Dalilin faduwar Abdulrasheed Maina a Abuja
Hakan na cikin wata sanarwa da Mai taimaka masa ta kafafen yaɗa labarai, Emmanuel Umahi Ekwe, ya tabbatar a shafinsa na Facebook inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata, 3 ga watan Faburairun 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa Maina ya rasa daidaituwarsa ne sakamakon rikicewar lafiyar gwiwa da bai samu magani ba, lamarin da ya sa ya faɗi tare da buga kansa a kan matakala.
An ce jami’an lafiya da ke wurin sun ba shi agajin gaggawa nan take, kafin daga bisani a ɗauke shi zuwa wani asibiti mai zaman kansa a Babban Birnin Tarayya Abuja domin samun kulawar gaggawa.

Source: Facebook
Wani halin Abdulrasheed Maina ke ciki?
A halin da ake ciki yanzu, an tabbatar da cewa Maina na ƙarƙashin kulawar likitoci sosai domin ganin ya dawo hayyacinsa ba tare da bata lokaci ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa bayan wani binciken lafiya na farko, ɗaya daga cikin likitocin da ke kula da shi ya ba da shawarar cewa a fara shirye-shiryen jigilar sa ta jirgin asibiti idan har lafiyarsa ba ta nuna alamun daidaituwa cikin ɗan gajeren lokaci ba.
Iyalan Maina tare da likitocinsa na ci gaba da sa ido kan yanayin lafiyarsa, inda iyalan suka roƙi ’yan Najeriya da su taya shi da addu’a, tare da mutunta sirrinsu a wannan lokaci mai muhimmanci.
Sanarwar ta ce, za a fitar da ƙarin bayani yayin da abubuwa ke ci gaba da faruwa bayan wani lokaci domin kwantar da hankulan mutane.
Maina na tone-tone kan Abubakar Malami
Kun ji cewa tsohon Shugaban kwamitin gyara fasalin fansho, Abdulrasheed Maina ya yi magana game da zargin da hukumomi ke yi wa tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami.
Ya ce kadarorin da ake alakanta wa Abubakar Malami SAN ba su kai kashi daya cikin hudu na abin da aka yi zargin ya wawure ba a lokacin da ya ke rike da mukamin.
Maina ya yabawa gwamnatin yanzu kan rikon gaskiya da bin doka, sabanin gwamnatin baya bayan an sako shi daga gidan yari da ya shafe shekaru takwas a garkame.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

