A Karon Farko bayan Abba Ya Koma APC, Kotu Ta Yi Zama kan Shari'ar Ganduje a Kano

A Karon Farko bayan Abba Ya Koma APC, Kotu Ta Yi Zama kan Shari'ar Ganduje a Kano

  • Babbar kotun jihar Kano ta yi zama kan shari'ar tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje, matarsa da wasu mutum shida
  • Wannan ne karo na farko da kotun ta yi zama bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC mai mulki
  • Lauyoyin sun yi barin bayanai, inda suka yi korafin cewa sun shigar da bukatu daban-daban amma kotu ba ta warware su ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Babbar Kotun Jihar Kano ta ɗage shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, tare da wasu mutane bakwai, zuwa ranar 15 ga Afrilu, 2026.

Ganduje, tsohon shugaban APC na kasa na fuskantar shari'a bayan gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta shigar da shi kara kan zargin almundahana da karkatar da kuɗaɗen jama'a.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun bi sawun dan kasuwar Kano, sun ɗauke shi a jihar Nasarawa

Ganduje.
Tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Source: Twitter

The Cable ta rahoto cewa Ganduje, tare da matarsa, Hafsat Umar, da ɗansa, Abdullahi Umar, na fuskantar tuhuma guda 11 da suka haɗa da zargin karɓar rashawa, haɗin baki, almundahana da karkatar da kuɗaɗen jama’a.

Sauran waɗanda ake tuhuma a shari’ar sun haɗa da Abubakar Bawuro, Jibrilla Muhammad, kamfanonin Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd, da Lasage General Enterprises Ltd.

Yadda zaman shari'ar Ganduje ya kaya

A zaman kotun na yau Talata, ɓangaren masu gabatar da ƙara ya sanar da kotu cewa a shirye suke a ci gaba da shari’ar.

Masu kara, watau gwamnatin Kano sun jawo hankalin kotu kan wata bukata da aka shigar ranar 24 ga Nuwamba, 2025, inda suke neman izinin gabatar da ƙarin hujjoji a kan waɗanda ake tuhuma.

Sai dai lauyoyi masu kare waɗanda ake tuhuma sun shaida wa kotu cewa akwai buƙatu da dama da har yanzu ba a yanke hukunci a kansu ba, waɗanda dole ne a fara warware su kafin a ci gaba da shari’ar.

Kara karanta wannan

Abin da Ganduje da makusantan Gwamna Abba suka tattauna a Abuja

Lauyoyin sun gabatar da korafe-korafe

Lauya Lydia Oluwakemi-Oyewo, wadda ke kare waɗanda ake tuhuma, ta ce sun shigar da wata buƙata a ranar 17 ga Yuli, 2025, inda suke neman dakatar da shari’ar gaba ɗaya.

Haka kuma, Adekunle Taiye-Falola, lauyan wanda ke kare wandanda ake tuhuma na uku da na bakwai, ya tunatar da kotu game da wata buƙata da ya shigar ranar 23 ga Mayu, 2025.

Shi ma Muhammad Shehu, lauyan wanda ake tuhuma na biyar, ya bayyana cewa sun shigar da bukatar sanar da kotu cewa suna neman dakatar da shari’ar a gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara.

Sai dai Faruk Asekome, lauyan wanda ake tuhuma na takwas, ya ce su a shirye suke a ci gaba da shari’ar, kamar yadda Trubune Nigeria ta ruwaito.

Gwamna Abba.
Gwamnan Kano, Abba Kabur Yusuf yayin ganawa da kwamishinoni a gidan gwamnati Hoto: Sanusi Bature
Source: Twitter

Bayan jin bayanan bangarorin, Mai Shari’a Amina Adamu-Aliyu, ta ɗage shari'ar zuwa ranar 15 ga Afrilu, 2024 domin sauraron dukkan buƙatun da ke gaban kotu da kuma ƙorafe-ƙorafen farko.

Kara karanta wannan

An 'gano' wanda Ganduje ya yi zargin ya tona masa asiri game da badakala a Kano

Gwamnatin Kano za ta yafe wa Ganduje?

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da cewa babu abin da zai dakatar da shari'ar cin hanci da rashawa kan tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje.

Kwamishinan yada labarai na Ibrahim Waiya, ya ce zarge-zargen cin hanci da ake yi wa tsohon gwamnan jihar, Dakta Umar Abdullahi Ganduje, na nan daram a gaban shari’a.

Sai dai a cewarsa, kotu ce kawai ta ke da hurumin ta tabbatar da shi a matsayin mai laifi, inda ya kara da cewa har yanzu babu wata kotu da ta tabbatar da laifin Ganduje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262