'Mutane Sun Tsere daga Gidajensu': Halin da Ake ciki a Gombe bayan Harin Ƴan Bindiga
- Sama da mutane 6,000 ne suka tsere daga gidajensu a jihar Gombe sakamakon hare-haren 'yan bindiga da suka lakume rayuka da dukiya
- Hukumomi sun fara tantance wadanda hare-haren suka shafa a masarautar Pindiga domin samar musu da abinci da matsugunan wucin gadi
- Har yanzu mutane hudu, ciki har da kananan yara, suna hannun masu garkuwa da mutane, wata guda bayan wani hari da aka kai Pindiga
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Gombe - Sama da mutane 6,000 ne suka tsere daga gidajensu biyo bayan munanan hare-haren 'yan bindiga a masarautar Pindiga dake jihar Gombe.
Hare-haren sun shafi Garin Galadima da wasu kauyuka dake karkashin karamar hukumar Akko, inda jama'a suka yi hijira domin tsira da rayukansu.

Source: Original
Gombe: Mutane sun tsere daga gidajensu
Mazauna yankin sun bayyana cewa harin na baya-bayan nan ya afku ne a ranar 23 ga watan Janairu, 2026 wanda ya tilasta musu barin garuruwansu, in ji rahoton Daily Trust.
Iyalan da abin ya shafa daga Garin Galadima, Lumbo, da Shulto yanzu haka suna gudun hijira a garuruwan Tumu, Kashere, da Pindiga, inda ke da aminci.
Masu gudun hijirar sun bayyana cewa 'yan bindigan sun shigo yankin su ne da yawa a kan babura, dauke da manyan makamai suna harbi kan mai uwa da wabi.
A kalla mutane uku ne aka tabbatar da mutuwarsu a lokacin harin, yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka daban-daban.
Matakin da gwamnatin Gombe ta dauka
Wadanda suka tsira suna zaune ne a gidajen dangi da abokan arziki, yayin da wasu ke fuskantar matsanancin hali na rashin matsuguni da abinci.
Gwamnatin Jihar Gombe ta bayyana damuwarta kan yadda wannan lamari ya janyo daruruwan mutane suka rasa muhallansu a lokaci guda.
Sakataren hukumar agajin gaggawa ta jiha (SEMA), Abdullahi Haruna Abdullahi, ya ce an hada gwiwa da hukumomin NEMA da NEDC domin tantance asarar.
Abdullahi ya bayyana cewa:
“Babban abin da muka sa a gaba yanzu shi ne samar wa wadanda aka tilasta su barin gidajensu wurin kwanciya, abinci, da ma matsuguni na wucin gadi.”
Ya kuma tabbatar da cewa suna tattaunawa da jami'an tsaro domin ganin an fatattaki 'yan bindigar yadda jama'a za su koma gonakinsu.

Source: Twitter
Halin da wadanda aka sace suke ciki
Duk da kokarin gwamnati, wata daya bayan harin garin Pindiga, har yanzu mutane hudu da aka sace suna hannun masu garkuwa da mutane.
Daga cikin wadanda ake garkuwa da su har da Zainab Mohammed yar shekara 16, da kananan yara Al’amin mai shekaru 11 da Fatima.
Amma kakakin 'yan sandan jihar, Buhari Abdullahi, ya sanar da cafke wasu mutane shida da ake zargi da aikata fashi da garkuwa da mutane a yankin Pindiga, in ji rahoton jaridar Tribune.
'Yan sandan sun ce sun gano makamai a hannun wadanda ake zargin, amma har yanzu ba a kai ga ceto wadanda aka sace ba.
Jami'an tsaro sun fafata da 'yan bindiga
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ‘yan sandan Gombe sun tabbatar da kashe wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, tare da kwato makamai da kuma ceto wasu mutane da aka sace.
Lamarin ya faru ne bayan ‘yan ta'addan sun kasa kai farmaki a wasu yankuna sakamakon tsauraran matakan tsaro, sai dai daga bisani suka kai hari a wani kauye.
Rundunar ‘yan sanda ta ce ana cigaba da bincike da farautar sauran ‘yan ta'addan da suka tsere, tare da bukatar jama’a su ci gaba da bayar da bayasai ga hukumomi.
Asali: Legit.ng


