Dakarun Sojoji Sun Nuna Bajinta, Sun Hana 'Yan Bindiga Sakewa a Sokoto
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai wani harin ta'addanci a wani kauye da ke jihar Aokoto a yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
- Dakarun sojoji ba su yi wata-wata ba suka kai daukin gaggawa bayan samun labarin harin da 'yan bindigan suka kai
- Jami'an tsaron sun yi artabu da 'yan bindigan inda suka samu nasarar fatttakarsu tare da kwato makamai a hannunsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Dakarun sojojin Najeriya karkashin rundunar Operation Fansan Yamma, sun samu nasara kan 'yan bindiga a jihar Sokoto.
Sojojin tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, sun dakile wani hari da ’yan bindiga suka kai kauyen Kola da ke karamar hukumar Salame ta jihar Sokoto.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Sojoji sun yi artabu da 'yan bindiga
Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 1 ga Fabrairu, 2026, da misalin karfe 6:15 na safe, bayan samun kiran gaggawa cewa dimbin ’yan bindiga dauke da manyan makamai sun mamaye kauyen.
A cewar majiyar, nan take aka tura sojojin Operation Fansan Yamma tare da jami’an sashen yaki da garkuwa da mutane zuwa yankin.
"Rundunar hadin gwiwar tsaro ta yi artabu da ’yan bindigar a wata musayar wuta da ta dauki wani lokaci."
"Daga karshe an rinjayi ’yan bindigar, wanda hakan ya tilasta musu suka tsere zuwa daji na kusa bayan sun yi asara mai girma."
- Wata majiya
An kwato makamai a hannun 'yan bindiga
Majiyar ta kara da cewa yayin gudanar da bincike a cikin dazukan da ke kewaye da yankin, jami’an tsaron sun kwato bindiga kirar AK-47 guda daya tare da alburusai guda 24, wadanda ake zargin na wani dan bindiga ne da aka kashe.
Haka kuma, rundunar ta samu nasarar kwato tumaki 48 da ’yan bindigan suka kwashe daga hannun mazauna kauyen a yayin harin.
Majiyar ta kara da cewa ba a samu asarar rai ba a bangaren sojoji ko na fararen hula ba a yayin harin.

Source: Original
Sojoji na ci gaba da sintiri
Ta kuma bayyana cewa ana ci gaba da zirga-zirgar sintiri domin karfafa kwarin gwiwa a yankin, yayin da aka sanya sojoji cikin shirin ko-ta-kwana domin sa ido kan duk wani dan bindiga da ya jikkata da ka iya neman mafaka.
Sojojin sun kuma kwantar da hankulan al’ummar Salame da makwabtanta, inda suka tabbatar musu da ci gaba da kasancewar tsaro a yankin, tare da bukatar su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai cikin lokaci.
'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a jihar Zamfara kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Mazauna yankin da aka kai harin sun ce maharan sun mamaye kauyen da misalin karfe 2:50 na rana, inda suka rika harbe-harbe ba kakkautawa, tuni wannan ya jefa jama’a cikin firgici.
Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da adadin mutanen da ba a tantance ba, inda suka tafi da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Asali: Legit.ng


