Malami Ya Sanar da Kotu Hanyoyin da Ya Samu Kudadensa a Shari'arsa da EFCC
- Tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan shari'a, Abubakar Malami, na fuskantar shari'a a gaban kotu
- Abubakar Malami ya gabatar da bukata a gaban kotu kan yunkurin da hukumar EFCC ke yi na kwace wasu kadarorinsa da ta ce an samu ta haramtacciyar hanya
- Tsohon Ministan ya sanar da kotu yadda ya samu kudadensa a tsawon shekarun da ya kwashe yana aiki da harkokin kasuwanci
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya yi bayanai a gaban kotu kan shari'arsa da EFCC.
Abubakar Malami ya shaidawa kotu cewa kadarorin da EFCC ke neman kwacewa a hannunsa, ya mallake su ne ta hanyoyi halastattu kuma bisa doka.

Source: Facebook
Jaridar Tribune ta kawo rahoton cewa Malami ya bayyana hakan ne yayin zaman kotu na ranar Litinin, 2 ga watan Fabrairun 2026.
Abubakar Malami ya yi bayani a gaban kotu
A cikin wata bukatar da tawagar lauyoyinsa karkashin jagorancin Joseph Daudu, SAN, ta shigar a madadinsa, Malami ya zargi EFCC da boye muhimman bayanai tare da yin bayanin da ba daidai ba, wanda hakan ya sa kotu ta bayar da umarnin wucin-gadi na kwace kadarorin.
Malami ya ce kudaden shigarsa da ribar da kasuwancinsa ke samarwa tsawon shekaru sun wadatar wajen nuna cewa kadarorin da ake son kwacewa an mallake su ne ta hanyar halal kuma bisa doka.
Daga ina Malami ya samu kudadensa?
The Punch ta ce Daudu ya shaida wa kotu cewa Malami ya bayyana dalla-dalla dukkan hanyoyin samun kudinsa a cikin takardun bayyana kadarori da ya mika wa CCB, ciki har da N374,630,900 daga albashi, kudin tafiye-tafiye, alawus da sauran kudade.
Takardun da aka gabatar wa kotu sun nuna cewa sauran kudaden shigar sun hada da:
"Alawus na zama mamba a kwamitoci da hukumomi kamar FJSC, hukumar shari’a ta babban birnin Abuja, kwamitin LPPC da wani babban kwamitin shugaban kasa."

Kara karanta wannan
Malami ya dauki mataki na hana EFCC kwace kadarori 57 da ya mallaka a Abuja, Kano
"N574,073,000 daga sayar da kadarori, Naira 10,017,382,684 a matsayin kudin shiga na kasuwanci. N2,522,000,000 a matsayin rance da aka bayar ga harkokin kasuwanci."
"N958,000,000 a matsayin kyauta daga abokai na kusa."
Joseph Daudu ya kuma bayyana cewa Malami ya samu N509,880,000 daga kaddamarwa da gabatar da littafinsa mai taken “Contemporary Issues on Nigerian Law and Practice, Thorny Terrains in Traversing the Nigerian Justice Sector: My Travails and Triumphs.”

Source: Facebook
Malami, wanda ya rike mukamin AGF a zamanin gwamnatin Muhammadu Buhari, yana neman kotu ta soke umarnin wucin-gadi da aka bayar kan kadarori uku daga cikin 57 da EFCC ta lissafo domin a kwace su zuwa hannun gwamnatin tarayya.
DSS ta fara bincikar Abubakar Malami
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar DSS ta fara bincike kan tsohon Ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami.
Hukumar DSS ta fara binciken ne bayan zargin an gano makamai da alburusai a gidansa da ke Birnin Kebbi a jihar Kebbi.
Majiyoyi sun bayyana cewa har yanzu ba a tantance adadi da irin makaman ba, amma sun ce sun isa su sa a kaddamar da cikakken bincike daga DSS.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
