Mutane 3 da ke da Karfi da Ikon Jan Akalar Gwamnatin Najeriya zuwa Matakin Nasara
- Farfesa Ibrahim Gambari ya jero mutane uku da suke da muhimmanci matuka wajen samun nasarar kowace gwamnatin Najeriya
- Tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar ya kafa hujja da wani abu da ya faru a mulkin Marigayi shugaba Muhammadu Buhari
- Ya ce nasarar duk wata gwamnatin tarayya da aka kafa a Najeriya ta dogara ne da yadda wadannan mutane suka tafiyar da ofisoshinsu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa (CoS), Farfesa Ibrahim Agboola Gambari ya bayyana mutanen da ke jan ragamar nasara ko akasin haka a gwamnatin Najeriya.
Gambari, wanda ya yi aiki da marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce nasarar kowace gwamnatin tarayya ko akasinta tana da alaƙa kai tsaye da wadanda aka nada a wadannan mukamai.

Source: Facebook
Farfesa Gambari, wanda kuma tsohon Jakadan Najeriya ne a Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na tashar Channels Television a daren Litinin.
Mutane 3 masu tasiri a gwamnatin Najeriya
Gambari ya ce nasarar kowace gwamnati ta dogara ne da mutanen da aka naɗa a muƙaman Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Shugaban Ma’aikatan fadar shugaban kasa (CoS) da kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF).
Ya ce idan waɗannan manyan jami’ai uku wato NSA, CoS da SGF suka yi amfani da ofisoshinsu yadda ya dace domin tallafa wa shugaban lasa, to lallai wannan gwamnati za ta yi nasara.
Ya kawo misali a lokacin da dangantaka ta yi tsami tsakanin Najeriya da Amurka a zamanin shugabancin Joe Biden, inda marigayi Shugaba Buhari ya aike shi tare da NSA na wancan lokacin domin ganawa da Biden, in ji Tribune Nigeria.
Gambari ya kafa hujja da mulkin Buhari
“Akwai mutane uku da zan iya faɗa maka a fili domin suna da matukar muhimmanci, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Shugaban Ma’aikata da Sakataren Gwamnatin Tarayya.
"Zan ba da misali daga abin da na sani. A zamanin mulkin Biden na Amurka, mun samu matsala kan ƙin sakin jiragen yaƙin Tucano da muka biya kuɗinsu amma aka riƙe su. Haka kuma, an saka Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da take hakkin addini.
"Ka san wa Buhari ya tura a ɓoye zuwa wurin Biden? Ni da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro. Mun je ba tare da hayaniya ba, amma mun samu sakamako mai kyau.
"An saki jiragen Tucano, kuma an cire Najeriya daga jerin ƙasashen da ake damuwa da su. Wannan yana nuna muhimmancin waɗannan ofisoshi da kuma yadda za a yi amfani da su cikin hikima da natsuwa don samun nasara.
- In ji Farfesa Gambari.

Source: Facebook
Yadda Buhari ya damu da tsaro
A wani labarin, kun ji cewa Ibrahim Gambari ya ce marigayi Buhari ya shiga damuwa sosai saboda rashin nasarar magance dukkannin matsalolin tsaro a Najeriya kafin ya bar mulki.
Tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Najeriya ya ce Buhari ya damu da matsalar tsaro, yana mai bayyana cewa tsohon shugaban bai ji dadin gaza dawo da tsaro ba.
Ya ce Buhari kan ji dadi idan ya tuna babu wani yanki da ke hannun Boko Haram, sai dai kuma bullar yan bindiga ta saka shi cikin damuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

